'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue

'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue

- 'Yan bindiga a jihar Benue sun afkawa wasu al'umma tare da kone gidaje da yawa a yankin

- 'Yan bindigan sun hallaka wani dan sanda tare da bankawa ofishi da motar 'yan sanda wuta

- Rundunar 'yan sanda a jihar ta Benue ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bata bada bayani ba

Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, a safiyar ranar Alhamis, sun kashe wani jami’in 'yan sanda tare da kona gidaje da dama ciki har da ofishin ‘yan sanda a yankin Tse Harga da ke karamar hukumar Katsina-Ala a jihar Benue.

An tattaro cewa yan bindigan da ake zargin yara ne ga babban mai kisan gilla, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da 'Gana', sun afkawa yankunan karkara da misalin karfe 4:00 na asuba sannan suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

An bayyana cewa, sun kone gidaje da dama tare da bankawa wani ofishi da motar 'yan sanda wuta.

Mazauna yankin, wadanda kuma suka tabbatar da cewa an kona wani ofishin 'yan sanda da gidaje da yawa, sun ce ba zasu iya tantance adadin mutanen da aka kashe ba.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina

'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue
'Yan bindiga sun sheke dan sanda, sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Benue Hoto: Nairaland Forum
Asali: UGC

Shugaban karamar hukumar ta Katsina-Ala, Alfred Atera, ya shaida wa wakilin Daily Trust ta wayar tarho cewa an kashe dan sanda daya a harin yayin da ofishin ‘yan sanda, motar 'yan sanda da gidaje da dama suka kone.

Atera ya bayyana cewa, saboda kalubalen tsaro a kananan hukumomin, matasa a Tse Harga sun kafa kungiyar 'yan banga kuma suna taka rawar gani don magance rashin tsaro a yankinsu.

“Yan bindigan sun nufi harin ne kan matasa wadanda suka tsoma kansu cikin kungiyar 'yan banga.

“Sun afkawa yankin (Tse Harga), sun kona ofishin 'yan sanda, motar ‘yan sanda sannan suka kashe wani dan sanda a wurin.

“Sun kuma kona gidaje da dama wadanda ba zan iya tantancewa yanzu ba. Amma ga mazauna yankin, ba wanda aka kashe,” ya bayyana.

Jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) na rundunar ta Benue, DSP Catherine Anene, a nata bangaren, ta tabbatar da kisan wani dan sanda a yankin da abin ya shafa.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

A wani labarin, Jaridar PM ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun sace wasu malamai da daliban makarantar fasaha ta kasa da ke Uromi a jihar Edo, An tattaro cewa 'yan bindigan sun afkawa makarantar ne a daren ranar Laraba inda suka yi awon gaba da wadanda suka sace.

Wannan ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, iyayen wadanda aka sace sun bayar da rahoton sun mamaye harabar makarantar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel