Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo

Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo

- 'Yan bindiga a jihar Edo sun sace wasu dalibai da malamansuda safiyar Alhamis da ba a san adadinsu ba

- Iyayen yaran tuni suka mamaye harabar makarantar tare da nuna rashin jin dadinsu game da satan

- Hukumar 'yan sanda a jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bata bada cikakken bayani ba

Jaridar PM ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun sace wasu malamai da daliban makarantar fasaha ta kasa da ke Uromi a jihar Edo,

An tattaro cewa 'yan bindigan sun afkawa makarantar ne a daren ranar Laraba inda suka yi awon gaba da wadanda suka sace.

Wannan ya haifar da tashin hankali tsakanin mazauna yankin.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, iyayen wadanda aka sace sun bayar da rahoton sun mamaye harabar makarantar.

Lokacin da aka tuntube shi ta wayar tarho, sabon mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP. Bello Kontongs ya tabbatar da rahoton.

Amma bai ba da cikakken bayani ba.

KU KARANTA: Ba za ta sabu ba, ba zamu yi hayar mayaka daga kasashen waje ba, Gwamnatin Buhari

Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo
Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo Hoto: The Sun Nigeria
Asali: UGC

"Na kuma ji labarin abin da ya faru tun daren jiya. Babu wani cikakken bayani har yanzu. Ina jiran babban jami'in da ke kula da yaki da satar mutane ya ba ni tabbacin cewa da zarar mun samu cikakken bayani za mu sanar da ku," in ji shi. .

Wani wakilin gidan Gwamnatin Jihar a ranar Alhamis, 11 ga watan Maris ya jawo hankalin mai bai wa Shugaban kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) game da lamarin satar.

Dan jaridar ya tambayi NSA ko yana cikin fargabar cewa dama ana iya yin kwatankwacin satar mutane a arewacin Najeriya a kudancin Najeriya.

NSA ya amsa, yana mai cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa abubuwan irin wadannan ba su yadu a fadin kasar ba.

Legit.ng ta shaida tattaunawar da NSA yayi da wakilan fadar Gwamnatin kai tsaye ta kafar YouTube.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

A wani labarin, Akalla, an sace mutane 55 a wasu hare-hare daban-daban da aka kai wa kauyukan Katsina.

‘Yan bindiga sun afka wa kauyen Katsalle da ke karamar Hukumar Sabuwa a daren Litinin, inda suka yi awon gaba da mutane 30, wadanda akasarinsu mata ne.

Wani mazaunin Katsalle ya shaida wa wakilin Daily Trust a waya cewa kusan 40 daga cikin ’yan bindigan sun isa kauyen da misalin karfe 12 na ranar Litinin, suna tafe akan babura.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.