Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina

Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina

- A kalla an sace mutane 55 a wasu yankunan jihar Katsina a yankin arewacin Najeriya

- An bayyana wadanda aka sacen cewa, mafi yawancinsu mata ne, kuma ba labarinsu har yanzu

- Ba a samu damar jin ta bakin shugaban rundunar 'yan sanda a jihar ba, saboda bai dauki waya ba

Akalla, an sace mutane 55 a wasu hare-hare daban-daban da aka kai wa kauyukan Katsina.

‘Yan bindiga sun afka wa kauyen Katsalle da ke karamar Hukumar Sabuwa a daren Litinin, inda suka yi awon gaba da mutane 30, wadanda akasarinsu mata ne.

Wani mazaunin Katsalle ya shaida wa wakilin Daily Trust a waya cewa kusan 40 daga cikin ’yan bindigan sun isa kauyen da misalin karfe 12 na ranar Litinin, suna tafe akan babura.

KU KARANTA: Buhari ya baiwa 'yan bindiga watanni 2 su mika wuya, in jiGwamnan Zamfara

Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina
Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina Hoto: Liberty
Source: UGC

“Lokacin da muka ga sun shigo, sai muka buya, muka yi kokarin jin ta bakin matan amma abin ya gagara saboda muna jin kukan yara na neman taimako, babu yadda za mu yi, akwai wani gida da suka saci mata goma,” in ji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata, rahotanni sun ce ’yan bindigan sun kai hari kauyukan Unguwar Tukur da Sabon Layin Mai Keke.

A Unguwar Tukur, sun sace mata 10, yayin da a Sabon Layin Mai Keke aka sace 15.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sai dai sashen Hausa na BBC ya ambato shi yana cewa suna jiran rahoton daga Jami’in ’Yan sanda na Shiyya ta Shiyyar.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora

A wani labarin, An samu rudani lokacin da jami'an runduna ta 7 ta sojojin Najeriya dake Maiduguri, suka gano kakin sojoji da katunan shaidar sojoji 145 da aka sauya a garin Marte da ke jihar Borno.

Lamarin ya faru ne ‘yan awanni kadan bayan da aka binne sojoji bakwai da aka kashe a wata arangama da suka yi da masu tayar da kayar baya a ranar 14 ga Fabrairu, 2021

A yayin harin, rahotanni sun ce maharan sun kona kayayyakin soji, da suka hada da motoci, tare da sace babura da kayayyakin abinci.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel