Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

- Jihar Katsina a arewacin Najeriya ta karbi allurar rigakafin Korona a daren ranar Laraba

- Jihar tuni dama ta fara yiwa wasu jami'an kiwon lafiya horo kan yadda za a gudanar da ita

- Ana sa ran fara yiwa gwamnan jihar ta Katsina kafin a fara yi wa ma'aikatan lafiya na gaba

A daren ranar Laraba ne jihar Katsina ta karbi kashin farko na rigakafin Korona.

Allurar rigakafin wacce ta haura sama da dubu dari, ta isa Filin jirgin saman Umaru Musa Yar’ardua a daren jiya.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar, Dr Shamsudeen Yahaya na daga cikin jami’an jihar da suka dauki nauyin karbar allurar rigakafin.

Ya kuma tabbatarwa Jaridar Punch ci gaban da aka samu na isowar allurar.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram

Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar
Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar Hoto: The Nation
Asali: UGC

“Alluran rigakafin sun iso yanzu (karfe 9.52 na dare) kuma muna gab da sauke kayan. Zan yi magana da ku nan gaba,” in ji shi.

An kuma gano cewa za a fara allurar rigakafin ga ma'aikatan lafiya a jihar nan take bayan an yi wa Gwamna Bello Masari allurar.

Ko dayake ba za a iya gano ainihin alluran da aka kawo ranar Laraba ba, wani babban jami’in gwamnati ya yi amannar cewa jihar za ta iya karbar tsakanin allurai 150,000 zuwa 160,000 na Korona.

Jami'in ya ce. “Dangane da yawan ma’aikatan lafiya na gaba da kuma wasu da muka aika zuwa Abuja, da alama za mu iya karbar allurai tsakanin 150,000 zuwa 160,000 kuma wannan zai kasance a kowane lokaci a mako mai zuwa.

“Abin da muke yi a yanzu shi ne tsarawa da kuma horo don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai. Mun horar da wasu ma’aikata kuma muna yin atisayen a ranar Alhamis.

"Za mu fara allurar rigakafin nan da nan da aka kawo mana."

KU KARANTA: Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita

A wani labarin, Najeriya, a makon da ya gabata ta samu isowar allurar rigakafin kwayar cutar Korona ta AstraZeneca a kokarin ta na yaki kwayar cutar.

Isowar allurar ke da wuya, gwamnatin kasar ta kaddamar da fara yin allurar ga ma'aikatan lafiya na sahun farko a kasar, kafin daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suka yi allurar a gaban kafafen yada labarai.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel