Ba za ta sabu ba, ba zamu yi hayar mayaka daga kasashen waje ba, Gwamnatin Buhari
- Gwamnatin shugaba Buhari a Najeriya ta shaida cewa, ba zata dauki hayar sojojin waje ba
- Gwamnatin ta yi ikrarin cewa tana da cikakkun kwararru domin yakar 'yan ta'adda a kasar
- Hakazalika, gwamnatin tace, sauye-sauye da ta yi a shugabancin tsaro zai kawo sauyi a kasar
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da tattaunawar shigo da sojojin haya na kasashen waje don yaki da masu tayar da kayar baya da sauran nau’ikan rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, The Nation ta ruwaito.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd), ne ya fadi haka a ranar Alhamis yayin wani taron a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce gwamnatin ta gwammace ta yi amfani da dukkanin rundunoni don kawar da yakin.
Monguno ya bayyanawa manema labarai cewa, Najeriya na da ma’aikata da kayan aiki don cimma nasara kan wadannan kalubalen tsaro na cikin gida.
KU KARANTA: Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo
“Ra’ayi da umarnin Shugaban kasa shi ne cewa ba za mu shigo da sojojin haya ba alhali muna da mutanenmu da za mu magance wadannan matsalolin. Muna da ma’aikata da kayan aiki, kuma Shugaban kasa ya bai wa sojojin wata sabuwar kwarin gwiwa,” inji shi.
Ya kuma ce, gwamnati ba za ta mika wuya ga yin zagon kasa da amfani da masu aikata laifi ba ta hanyar muzgunawa 'yan kasa ba tare da wani laifi ba, ya kara da cewa abinda ya fi dacewa shine ta girka duk karfin da ya dace don kawar da masu laifin.
Ya kara da cewa, sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya yi a tsarin shugabancin tsaro “ya ba mu kwarin gwiwa cewa abubuwa za su daidaita, ta yadda duk abin da za mu yi game da tsaron Najeriya za su yi daidai da bukatun mutane.”
KU KARANTA: Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar
A wani labarin, Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta dauki hayar sojojin kasashen waje domin yakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram.
Majalisar ta yanke wannan shawara ne sakamakon wani kudiri da Abdulkadir Rahis ya gabatar a ranar Laraba.
Kudirin na Mista Rahis ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake tsara dabarun yaki da masu tayar da kayar baya.
A gefe guda, Mansur Soro, ya gabatar da kwaskwarima ga kudirin, yana mai yin kira ga gwamnati da ta yi la’akari da mayakan kasashen waje da ake biyansu kudi a yaki da ta’addanci.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng