Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram

Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram

- Majalisar wakilai a Najeriya ta shawarci shugaba Buhari kan hayar sojojin kasashen waje

- Majalisar ta bayyana hakana a matsayin mafita ga yakar 'yan Boko Haram a yankin Arewa

- A shekarar da ta gabata, gwamna Zulum ya yi irin wannan kira ga gwamnatin Buhari don samun mafita

Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta dauki hayar sojojin kasashen waje domin yakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne sakamakon wani kudiri da Abdulkadir Rahis ya gabatar a ranar Laraba.

Kudirin na Mista Rahis ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake tsara dabarun yaki da masu tayar da kayar baya.

A gefe guda, Mansur Soro, ya gabatar da kwaskwarima ga kudirin, yana mai yin kira ga gwamnati da ta yi la’akari da mayakan kasashen waje da ake biyansu kudi a yaki da ta’addanci.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona

Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram
Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Wannan kudurin na zuwa ne sakamakon irin wannan kira na Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, wanda a yayin taron kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas kwanan nan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta koma amfani da sojojin haya na kasashen waje.

Gwamna Zulum a watan Nuwamba na shekarar 2020 ya tabo batun hayar mayaka da ake biyansu daga kasashen waje, manufar da aka yi la’akari da ita a karkashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan.

Gwamnatin Jonathan ta yi amfani da kamfanin Kebabbun Ayyuka, Horarwa, Kayan aiki da Kariya, (STTEP), wani kamfanin Afirka ta Kudu don yaki da masu tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabas

Sai dai, shugaba Buhari na adawa da manufar, yana mai bayyana ta da "abin kunya."

A cikin shekarar 2018, Eeben Barlow, wanda ya kafa STTEP, a cikin wani sakon da ya wallafa a Facebook, ya bayyana yadda shugaba Buhari, a matsayinsa na mai adawa, ya ki amfani da sojojin haya na kasashen waje da gwamnatin wancan lokacin ta yi.

Mista Barlow a cikin sakon ya yi Allah wadai da ikirarin da gwamnatin ta yi cewa an ci karfin kungiyar a fasaha.

Mista Rahis, a cikin kudurin da ya gabatar, ya yi karin haske game da karuwar hare-hare a Maiduguri, musamman harin ranar 23 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka 16.

Ya lura cewa "harin ya kasance daya daga cikin mafiya tsoro yayin da 'yan ta'addan suka harba nakiyoyi da gangan zuwa cikin garin wanda ya yi sanadiyyar mummunar barna a kan jama'a."

KU KARANTA: Bayan taron addu'a, Sarkin Kano yace 'yan Najeriya da su amince da rigakafin Korona

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan bindiga a Zamfara wa'adin watanni biyu su mika wuya, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya fada a cikin wani shiri da yammacin Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya ce shugaban ya kuma bayar da umarnin tura dakaru 6,000 domin murkushe 'yan ta'addan idan suka kasa mika makamansu.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne 'yan sa'o'i kadan bayan da sarakunan gargajiya a jihar suka fada wa shugabannin hafsoshin tsaro, wadanda suka kawo ziyara jihar, cewa akwai 'yan fashi sama da 30,000 a dazukan Zamfara.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.