'Yan ta'adda sun shiga Maiduguri, zakakuran sojin Najeriya sun yi musu 'dakan gumba'
- A daren Talata ne mayakan ta'addanci na Boko Haram suka kai mummunan hari Maiduguri
- An gano cewa 'yan ta'addan basu sha da kyau ba a hannun zakakuran dakarun sojin Najeriya
- Salon harin Boko Haram ya fara sauya salo inda suke kai farmaki babban birnin jihar Borno
Dakarun sojin Najeriya sun yi martanin gaggawa a harin da mayakan ta'addanci suka kai a daren Talata har babban birnin Maiduguri, jihar Borno.
Harin ya zo ne bayan makonni kadan da aka kaiwa Maiduguri mummunan hari inda 'yan ta'addan suka ratsa jami'an tsaron da ke birnin suka wurga bam wanda ya halaka a kalla mutum 15.
HumAngle ta gano cewa mazauna garin a daren Talata sun shiga dimuwa bayan da suka ji karar harbin bindigogi da tashin abubuwa masu fashewa.
KU KARANTA: Mun baiwa 'yan bindiga buhu 7 na shinkafa don tseratar da rayukanmu, Jami'in kwastam
Harin da aka kai Maiduguri an gano ya faru ne a wurin da ya auku a ranar 23 ga watan Fabariru.
HumAngle ta gano cewa dakarun da aka tura yankin sun gaggauta mayar da martanin mummunan harin.
Har yanzu ba a san yawan wadanda harin ya shafa daga dakarun har 'yan ta'addan.
A ranar 5 ga watan Maris ne jaridar HumAngle ta ruwaito cewa Boko Haram ta samo sabbin salo na kai ta'addancinta har cikin babban birnin jihar Borno, wato Maiduguri.
KU KARANTA: Hotuna: Hafsoshin tsaro sun dira jihar Zamfara, sun shiga ganawa da Matawalle
A wani labari na daban, sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya cika shekara daya a kan karagar mulkin dabo.
Domin tunawa da ranar da ya hau karagar mulkin, babban basaraken ya jagoranci addu'a ta musamman a babban masallacin jihar Kano.
Kamar yadda masarautar ta wallafa a shafinta na Twitter, "Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci addu'ar cika shekara 1 a matsayin sarkin Kano a safiyar yau Talata, 9 ga watan Maris 2021."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng