Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

- Shugaba Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin wata 2 su ajiye makamai a jihar Zamfara

- Shugaban kasar ya kara da tura karin dakarun soji 6000 jihar domin murje 'yan ta'addan

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya sanar da hakan a jawabinsa na daren Talata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa 'yan bindigan Zamfara watanni biyu to mika makamai, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da yammacin Talata.

Matawalle yace shugaban kasan ya bada umarnin tura dakaru 6,000 domin murje 'yan bindiga idan suka ki mika makamansu, Daily Trust ta wallafa.

Gwamnan ya sanar da hakan sa'o'i kadan bayan sarakunan gargajiya sun sanar da shugabannin tsaro da suka ziyarci jihar cewa akwai sama da 'yan bindiga 30,000 dake dajikan jihar.

KU KARANTA: Bidiyo: Sunday Igboho ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga 'yan sanda, soja da DSS

Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai
Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Wannan umarnin da shugaban kasa ya bada ya biyo baya ne bayan kusan mako daya da hana jiragen sama bi ta jihar tare da haramta hakar ma'adanai domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.

A jawabin da yayi na daren jiya, gwamnan Zamfaran yace ya kwashe kwanaki hudu a Abuja inda yake bayyanawa shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki halin da jiharsa ke ciki ta fannin tsaro.

KU KARANTA: Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki

A wani labari na daban, jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona na AstraZeneca a ranar Talata. Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin martani na jihar ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.

"Jihar Kano ta shirya karbar rigakafi. An sanar da NPHCDA cewa Kano za ta karba kasonta a yau. Mun yi tsammanin samunsa a jiya amma yau zamu samu aka ce," yace.

Ya ce jihar ta shirya kaso 70 na shirin fitar dashi tare da fara yi wa jama'a rigakafin bayan ta karba.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng