Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa

Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa

- Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa ba zai yi yaki da mutane a jagorancinsa ba

- A cewarsa, hukumar zata dukufa ne wajen yakar cin hanci da rashawa da dawo da kudade

- Hakazalika ya bayyana hanyar da zai bi domin zamanantar da ayyukan hukumar nan gaba

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ya ce a karkashin jagorancinsa, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa za ta himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa, The Cable ta ruwaito.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada Bawa a watan Fabrairu kuma daga baya majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ta EFCC.

Da yake jawabi a ranar Juma'a lokacin da ya hau kujerar a hukumance, Bawa ya yi alkawarin jan ragamar hukumar zuwa ga bin diddigi da binciken sirri.

Ya ce zai kirkiro da cikakken iko na hukumar leken asiri da za ta jagoranci tattara bayanan sirri, wadanda zasu tabbatar da kwararan matakan yaki da cin hanci da rashawa.

Bawa ya kuma yi alkawarin sauya fasali a tsarin hukumar na yaki da cin hanci da rashawa, wanda zai mai da hankali kan yaki da rashawa, ba mutane ba.

KU KARANTA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna

Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa
Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

“Zamu zamanantar da ayyukan mu, kuma zamu kirkiro da wani sabon shugabanci mai cikakken iko wanda zai bamu damar tattara bayanan sirri ta yadda zamu zama masu himma wajen yakar laifukan tattalin arziki da na kudi.

"Kuma ta yin hakan, za mu kuma bai wa gwamnati shawarwari masu inganci da za su haifar da kyakkyawan shugabanci,” in ji Wilson Uwujaren, kakakin EFFC, ya ce.

“Akwai bambanci tsakanin fada da cin hanci da rashawa da fada da mutane masu rashawa; kuma a ci gaba, za mu kasance masu himma wajen yaki da laifukan tattalin arziki da na kudi.

“Ga abokan hadin gwiwarmu da ke fadin kasar nan, za mu ci gaba da aiki tare da ku. Za mu ci gaba da musayar bayanan sirri, don ganin an dawo da dukiyar da aka sace ta kasar nan don ci gaban mu baki daya.

“Amma duk wadannan, za mu yi su ne kamar yadda aka san EFCC da yin abubuwan ta. Abubuwan da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da dokokin kasar nan suka shimfida, sun kasance sune jagora a garemu.”

Bawa ya karbi aiki ne daga hannun Mohammed Umar wanda ke rike da mukamin tun watan Yulin shekarar 2020 bayan dakatar da Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar, kan zargin cin hanci da rashawa.

A lokacin mika jawabin, Umar ya bayyana kwarin gwiwar cewa Bawa zai gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

KU KARANTA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna

A wani labarin, Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bukaci masu yi wa sabon shugaban da aka nada, Abdulrasheed Bawa, fatan alheri da su daina biyan kudi don taya shi murna, The Nation ta ruwaito.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ta Wilson Uwujaren ya fitar a shafin Twitter @OfficialEFCC, EFCC ta ce dukiyar da aka kashe kan sakonnin taya murnar za a iya kaiwa ga yin abubuwan da suka dace, kamar tallafawa 'yan gudun hijira.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel