Kotu ta ci gaba da zaman shari'ar Ganduje kan batun bidiyon dala

Kotu ta ci gaba da zaman shari'ar Ganduje kan batun bidiyon dala

- A ci gaba da sauraran kara kan batun sanya dala a aljihu da aka gano Ganduje nayi, yau sun yi zaman shari'a

- Lauyoyin Jaafar Jaafar sun koka kan ganin sabbin lauyoyi da Ganduje ya turo gaban kotun

- Alkalin kotun, ya dage karar bayan watsi da kokensu zuwa wani lokaci don ci gaba da zama

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Titin Miller na Unguwar Bompai, a yau Litinin ta ci gaba da sauraron shari’ar bidiyon zuba daloli a cikin aljihu da ake zargin an nado gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje yana yi.

A shekarar 2018 aka wallafa wani bidiyon gwamna Ganduje yana sanya daloli a cikin aljihu wanda ake zargin cin hanci ne daga wani dan kwangila a Jihar, lamarin da makarraban gwamnan suka ce bidiyon ba sahihi ba ne kuma an yi hakan ne kurum dan a bata shi.

Sai dai mai jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar wanda ya fitar da bidiyon a baya, ya dage a kan cewa bidiyon ya inganta kuma babu wani coge ko kage a cikinshi.

KU KARANTA: Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona

Kotu ta ci gaba da zaman shari'ar Ganduje kan batun bidiiyon dala
Kotu ta ci gaba da zaman shari'ar Ganduje kan batun bidiiyon dala Hoto: The Will Nigeria
Asali: UGC

A yayin zaman kotun na yau karkashin jagorancin Mai Shari’a Sulaiman Baba Na Malam, lauyan Jaafar Jaafar da na jaridar Penlight sun soki yadda masu wakiltar bangaren Ganduje suka kawo sabbin lauyoyi sabanin wadanda aka fara shari’ar da su tun farin shari'ar.

Aminiya ta samu cewa, Mai Shari’a Na Malam ya yi watsi da sukar lauyoyin masu karar da suka yi, inda kuma ya sake dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Afrilun 2021.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom mai tushe a Kanon Dabo ta ruwaito, ta ce lauyoyin gwamna Ganduje sun ce ba sababbin lauyoyi suka kawo ba, illa iyaka kari ne a kan lauyoyin da suke kare su.

Shi kuwa lauyan Jaafar Jaafar U. U Ete cewa ya yi, sun yi sukar ne ganin yadda aka zo da sabbin fuskoki a madadin Barista Nura Ayagi da aka fara shari’ar da shi tun farko.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

A wani labarin, Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai ba gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya bayyana korar tasa a matsayin "fita mai mutunci".

Gwamna Ganduje ya kori Yakasai daga aiki ne saboda wani jawabi da ya yi na kira mai matukar muhimmanci ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da korarsa a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel