Sa'adat Aliyu: Ƴar Kano ta ƙera manhajar shigar da ƙorafin fyaɗe
- Matashiya haifafar jihar Kano ta ƙera manhajar android na kai rahoton fyaɗe
- Saadat Aliyu ta ce kowa zai iya Playstore domin sauke manhajar 'Helpio App'
- Matashiyar wacce ta kafa kamfanin Shamrock ta ce tana aiki kan wani manhajar da zai amfani mata da sauran jama'a
Wata matashiya haifafar jihar Kano, Saadat Aliyu ta ƙera manhajar android mai suna 'Helpio App' domin kai rahoto kan fyaɗe, Channels Television ta ruwaito.
An kaɗamar da 'Helpio App' a playstore a ranar 6 ga watan Agustan 2020.
Saadat Aliyu wacce ta kafa Shamrock Innovations, cibiyar Fasaha ta Mata da Matasa a Kano ta ce kowa na iya zuwa Playstore ya sauke manhajar a wayarsa.
DUBA WANNAN: Ranar mata ta duniya: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari
"Za ka iya zuwa Playstore, ka nemo shi sannan ka sauke a wayarka. Daga nan sai ka yi rajista da imel ɗin ka cikin harshen Hausa ko Ingilishi," kamar yadda ta shaidawa Channels Television a ranar Litinin.
"Kawo yanzu kungiyar tallafawa wadanda aka ci zarafinsu, marayu da marasa galihu (ISSOL) da wata ƙungiyar na tallafawa gajiyayu, kare hakkin yara da walwalarsu (EDCRAW) sun yi rajista a manhajar."
Ta ce ta fara koyon fasahar sadarwa ne daga wurin ɗan uwanta a lokacin tana ajin ƙaramar sakandare daga bisani ta koya da kanta har ta zama mai ƙera manhaja.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido
Matashiyar ta ce nan ba da dadewa ba za ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar ta mai alaka da fasaha da kuɗi da ake fatan zai taimakawa mata da sauran jama'a.
A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.
An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.
JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng