Attajirin Yariman Saudiyya zai siya ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Faransa
- Yarima Abdullah bin Mosaad na kasar Saudiyya zai siya kungiyar kwallon kafa ta Chateauroux a kasar Faransa
- A halin yanzu Abdullahi yana da kungiyoyi da suka hada da Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United a UAE
- Yarima Abdullahi ya ce yana fatar kungiyar za ta farfado nan gaba duk da cewa yanzu tana kasar tebur na gasar kwallon Faransa
Yariman Saudiyya masoyin 'kwallon kafa da kudi', Yarima Abdullah bin Mosaad yana dab da mallakar kungiyar kasar Faransa ta Chateauroux, The Punch ta ruwaito.
Yariman wanda ya mallaki kungiyoyin Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United a UAE yana daf da kara sabuwar kungiya kan wadanda ya ke da su.
DUBA WANNAN: Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi
"Mun dade muna sha'awar Chateauroux, muna yi nisa da tattaunawa," Yarima Abdullahi ya shaidawa AFP cikin hirar Zoom.
"Kungiyar na cikin mayucin hali a mataki na biyu amma ina sa ran za ta farfado a nan gaba."
A halin yanzu Chateauroux tana kasar tebur na gasar kwallon kafa na Faransa inda ta samu nasarori hudu cikin wasanni 28 da ta buga.
Akwai yiwuwar za ta iya fadawa mataki na uku.
Yariman, wanda ya taba jagorancin bangaren wasanni a gwamnatin Saudiyya ya bada umurnin a siya masa kungiyar ta Chateauroux don hada ta cikin jerin kungiyoyin da ya mallaka.
"Ina kaunar wasanni da kudi," in ji Yariman mai shekaru 56 da aka kiyasta arzikinsa $240,000 miliyan.
KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido
"A lokacin da na saka hannun jari a Ingila da Belgium, na yi farin ciki. Amma Faransa daban ne saboda kasar na tuna min kuruciya ta.
"Akwai ababe da yawa da na ke tunawa a kasar da dan uwa na (yarima) Abdulrahman a can aka haife shi.
"Na san Chateauroux babu nisa daga Paris (kimanin kilomita 270) wani dalilin da zai sa in yi farin ciki idan na tafi Faransa bayan zuwa wurin cin abinci, shan shayi da wurin mike kafa."
A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.
An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.
JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng