Rigakafin corona ta isa jihar Ogun, Gwamna Dapo Abiodun ya tabbatar

Rigakafin corona ta isa jihar Ogun, Gwamna Dapo Abiodun ya tabbatar

- Kwanaki kaɗan bayan isowar allurar rigakafin corona, gwamnatin tarayya ta fara rabawa zuwa jihohin kasar nan

- Gwamnan jihar Ogun ya tabbatar da isowar allurar jihar sa a yau

- Jihar Ogun ta zama ta farko da aka fara turama rigakafin a duk faɗin jihohin ƙasar nan

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya tabbatar da isowar allurar rigakafin cutar corona jihar sa. Punch ta ruwaito.

Gwamanan yace sun amshi wani kaso daga gwamnatin tarayya na allurar Astrazeneca.

KARANTA ANAN: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido

Dapo Abiodun, ya bayyanar da hakan a shafinsa na twitter inda ya ƙara da cewa jiharsa ita ce ta farko data amshi rigakafin a cikin jihohin ƙasar nan.

"Mun amshi allurar rigakafin Astrazeneca a ofishi na dake Oke- Mosan, a babban birnin jihar, Abeokuta. Jihar mu itace ta farko da rigakafin ta iso mata a faɗin kasar nan," inji gwamnan.

A kwanakin baya gwamnan ya bayyana cewa jiharsa ta shiryawa isowar rigakafin tun sanda ta shigo ƙasar, kuma ta shirya wurin da zata ajiye ta.

Rigakafin corona ta isa jihar Ogun, Gwamna Dapo Abiodun
Rigakafin corona ta isa jihar Ogun, Gwamna Dapo Abiodun Hoto: @dabiodunMFR
Source: Twitter

Ya kuma ƙara da cewa, matsalolin tsaro da ake fuskanta a jihar ba zasu hana gudanar da rigakafin ba har sai ta isa ga waɗanda ya kamata.

"Mun saka wutar lantarki mai amfani da hasken rana wadda zata sanyaya wurin da zamu aje rigakafin da ta iso kasarmu a yanzu, kuma zamu fi bawa ma'aikatan lafiya muhimmanci wajen gudanar da allurar," Inji gwamnan.

KARANTA ANAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Gwamnan ya ƙara da cewa, rashin tsaro da muke fama dashi a jihar nan bazai hana mu gudanar da allurar rigakafin ba.

Da yake magana akan rashin tsaron, gwamnan yace kwanan nan zamu ƙaddamar da jami'an tsaron mu da muka sama suna 'Amotekun Corps'.

A wani labarin kuma Jami’an NDLEA sun bankado miyagun kwayoyi da aka boye a fadar wani babban Basarake

Hukumar NDLEA ba ta iya bayyana sunan wannan basarake da aka samu kwayoyin a fadarsa ba.

NDLEA ta shigo makon nan da gagarumar nasara kan masu safarar kwaya inda tsamu nasarar yin wannan babban kamu.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit

Online view pixel