Jami’an NDLEA sun bankado miyagun kwayoyi da aka boye a fadar babban Basarake

Jami’an NDLEA sun bankado miyagun kwayoyi da aka boye a fadar babban Basarake

- NDLEA ta shigo makon nan da gagarumar nasara kan masu safarar kwaya

- Jami’an Hukumar sun gano miyagun kwayoyi da aka boye cikin fadar Sarki

- An samu fiye da 70gms na kwayoyin Cocaine da Heroine a fadar Basaraken

Wasu jami’an hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya sun yi nasarar gano wasu kwayoyi da aka boye a fadar Sarki a Anambra.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami’an NDLEA na jihar Anambra sun samu hodar iblis wanda aka fi sani da ‘Cocaine’ da Heroine a fadar wannan basarake.

Kamar yadda hukumar ta bayyana a ranar Litinin, an samu giram 58.5 na hodar iblis, da girma 13.9 na Heroine a gidan wani fitaccen basarake a jihar Anambra.

Hukumar NDLEA ba ta iya bayyana sunan wannan basarake da aka samu kwayoyin a fadarsa ba.

KU KARANTA: NDLEA ta kama hodar ibilis ta N30bn da aka shigo da ita daga Brazil

Shugaban hukumar NDLEA na reshen jihar Anambra, Muhammadu Misbahu Idris, ya fitar da sanarwa ya ce su na bincike domin gano yadda abin da ya auku.

Misbahu Idris ya ce dogaran fadar Sarki su na ba jami’an NDLEA hadin-kai da nufin a samu a gano wanda ya shigo da kwayoyin har cikin fadar Mai martaba.

“Ana cigaba da gudanar da bincike domin gano yadda aka boye miyagun kwayoyin a cikin fadar, kuma dogarai su na taimaka wa wajen gano dillalin kwayoyin.”

Duk a yau ne kuma NDLEA ta kama wani mutumi da ya yi guzurin giram 500 na hodar iblis zai tafi kasar UAE. An boye wannan kwayoyi ne cikin wasu kaya.

KU KARANTA: Buba Marwa ya karbi ragamar shugabancin NDLEA

Jami’an NDLEA sun bankado miyagun kwayoyi da aka boye a fadar babban Basarake
Buba Marwa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Har ila yau, an damke wani mutumi dauke da methamphetamine duk a filin jirgi, zai nufi kasar Sin.

Kun samu rahoton yadda aka yi ram da kwayoyin Naira Biliyan 60 bayan shugaba Muhammadu Buhari ya nada Janar Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA.

Hukumar NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyii a Najeriya ta ce ta karbe kwayoyi na sama da Naira biliyan 60 a fadin Najeriya a cikin makonni shida rak.

Sabon shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa ya nuna da gaske ya ke yi, ya yi kira ga jagororin addini da gargajiya su bada gudumuwar yakar annobar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel