Sojin sama sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga, Rufai Maikaji da mukarrabansa

Sojin sama sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga, Rufai Maikaji da mukarrabansa

- Sojin saman Najerya sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga a wani samamen da suka kai

- 'Yan bindigan sun taru a wani mugun daji da ke jihar Kaduna lokacin da sojin suka musu ruwan wuta

- Gwamnan Kaduna ya sanar tare da sake jaddada cewa babu sasanci tsakaninsa da 'yan bindiga kamar yadda wasu takwarorinsa ke yi

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kisan da aka yi wa daya daga cikin shugabannin kuma gagararren dan bindiga mai suna Rufai Maikaji tare da sama da 'yan bindiga dari dake karkashinsa.

Labarin mutuwar Maikaji ta fasu ne bayan kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da ita a wata takarda.

Kamar yadda takardar ta sanar, Maikaji tare da daruruwan 'yan bindiga sun sheka lahira bayan samamen da sojin sama suka kai a dajin Malul da ke karamar hukumar Igabi ta jihar..

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba

Da duminsa: Sojin sama sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga, Rufai Maikaji
Da duminsa: Sojin sama sun sheke gagararren shugaban 'yan bindiga, Rufai Maikaji. Hoto daga @DefenceInfong
Asali: UGC

Wani sashi na takardar na cewa: "Samamen da sojin saman Najeriya suka kai a karshen watan Fabrairun da ta gabata sun yi nasarar halaka Rufai Maikaji da gungun 'yan bindiga dake karkashinsa.

"'Yan bindigan sun tsere zuwa kauyen Anaba da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan ganin sojojin kasa. Na saman sun gaggauta yi musu ruwan wuta wanda hakan ya kawo karshen Rufai Maikaji da mukarrabansa."

KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana cewa sun yanke hukuncin yin sasanci shi da takwaransa na jihar Bauchi domin samun hanyar shawo kan lamurran da ke ci wa mutane kwarya a kasar nan.

Kafin nan, dukkan gwamnonin sun dinga tada kayar baya inda suke caccakar junansu a kan rikicin makiyaya da manoma, Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Ortom ya zargi Mohammed da bayyana goyon bayansa ga Fulani da ke yawo da makamai yayin da ya zargesa da zama cikin kungiyar 'yan ta'addan da ke addabar kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel