Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara

Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara

- Jam'iyyar PDP ta zargi APC da yunkurin kulle-kullen kwace ragamar mulkin jihar Zamfara akan matsalar tsaro dake addabar jihar

- Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ne ya gabatar da wadannan korafin na jam'iyyar ta wata takarda a ranar Laraba

- Dama tun bayan 'yan bindiga sun saci daruruwan daliban GGSS Jangebe dake jihar Zamfara aka tsananta tsaro a jihar

Jam'iyyar PDP ta zargi APC da kulle-kullen kwace jihar Zamfara sakamakon rashin tsaron da yake addabar jihar a cikin kwanakin nan.

Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya gabatar da korafin a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Dama gwamna Bello Matawalle na jam'iyyar PDP ne yake shugabantar jihar dake arewa maso yamma, Premium Times ta wallafa.

'Yan bindiga sun saci daruruwan daliban GGSS Jangebe dake jihar a ranar Juma'ar da ta gabata. Amma sun sakesu da safiyar Talata.

KU KARANTA: Abinda yasa muke kai yara karatu kasashen ketare, Kwankwasiyya

Rashin tsaro: PDP na zargin APC ta kitsa yadda za ta kwace Zamfara
Rashin tsaro: PDP na zargin APC ta kitsa yadda za ta kwace Zamfara. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

A ranar, gwamnatin tarayya ta hana tashin jirgin sama a jihar da kuma dakatar da hako ma'adanai a jihar sakamakon rashin tsaron.

Kafin faruwar lamarin Zamfara, sai da 'yan bindiga suka yi garkuwa da akalla dalibai maza 27 na Kagara dake jihar Neja a makonni uku da suka gabata.

Haka kuma sun taba satar fiye da dalibai 600 na Kankara dake jihar Katsina a karshen watan Disamban 2020.

Daga jihar Neja har Katsina, gwamnonin jam'iyyar APC ne suke shugabatar jihohin.

Sakamakon hakan ne jam'iyyar PDP ta zargi APC da kulle-kulle a jihar bisa wata manufar siyasa bayan sanya dokar hana tashin jirgin sama a jihar.

"Jam'iyyarmu ta nuna rashin amincewarta da yunkurin gwamnatin APC wurin kulle-kullen kwace jihar Zamfara wacce gwamna Bello Muhammad Matawalle yake shugabanta don nuna cewa ba ya aikinsa alhalin gazawar gwamnatin tarayya wacce take karkashin jam'iyyar APC ne ya janyo rashin tsaron jihar," cewar Ologbondiyan.

KU KARANTA: Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

A wani labari na daban, gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana cewa sun yanke hukuncin yin sasanci shi da takwaransa na jihar Bauchi domin samun hanyar shawo kan lamurran da ke ci wa mutane kwarya a kasar nan.

Kafin nan, dukkan gwamnonin sun dinga tada kayar baya inda suke caccakar junansu a kan rikicin makiyaya da manoma, Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Ortom ya zargi Mohammed da bayyana goyon bayansa ga Fulani da ke yawo da makamai yayin da ya zargesa da zama cikin kungiyar 'yan ta'addan da ke addabar kasar nan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng