'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba

'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba

- Adamu Garba, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya caccaki 'yan kudancin Najeriya

- Garba ya kira masu nuna bangarancin yanki idan laifi ya tashi da munafukai masu kushe 'yan ta'addan arewa

- Dan siyasan yace babu banbanci tsakanin Abubakar Shekau, Nnamdi Kanu da kuma Sunday Igboho

Tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Adamu Garba ya je kafar sada zumunta inda ya bayyana takaicinsa a kan yadda jama'a ke nuna ra'ayinsu dogaro da yankin mutum.

Garba ya kwatanta mutanen kudancin Najeriya da munafukai, ya ce basu iya kushe duk wani laifi da mutanen yankinsu suka yi amma su dinga kushe na arewa, Vanguard ta wallafa.

"Alamu suna nuna cewa muna da baiwar matsayi, mutunci da kuma arziki kuma muna da masu saka bama-bamai da alburusai a arewa," Garba yace.

KU KARANTA: Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba
'Yan Boko Haram da 'yan bindiga masu gwagwarmayar nemawa arewa 'yanci ne, Adamu Garba
Asali: Original

"Kun ga munafuncin da ke cike da yadda ake shawo kan matsalolin Najeriya?"

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, Garba ya alakanta wasu ayyukan 'yan bindiga da suka hada da satar yara, kai hari kauyuka da kashe-kashe da irin ayyukan Ralph Uwazuruike da Nnamdi Kanu.

Dukkansu suna ikirarin cewa masu gwagwarmaya ne kuma an saka musu da kujerun siyasa, kwangiloli da kuma mayar da su jarumai a yankin kudu maso gabas.

Garba yace babu banbanci tsakanin Abubakar Shekau da Nnamdi Kanu da Sunday Igboho.

KU KARANTA: 'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe

A wani labari na daban, kungiyar gamayya ta masu siyar da kayan abinci tare da masu siyar da shanu ta Najeriya (AUFCDN) ta ce ta gwammace kayan abinci su lalace da ta cigaba da lamuntar harin da ake kaiwa mambobinta na kudu.

Awwalu Aliyu, jami'in kungiyar wanda ya tattauna da TheCable a Kano ranar Talata, ya ce wannan hukuncin ba na saka 'yan kudu a yunwa bane, amma na nuna rashin jin dadi da yadda ake kaiwa mambobinsu hari ne.

Aliyu ya zargi cewa wasu daga cikin mambobinsu da gangan aka kashesu tare da barnatar musu da dukiyoyinsu ballantana yayin zanga-zangar EndSARS da kuma rikicin kasuwar Shasha a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng