Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom

Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom

- Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya ce ganin halin tsaron da kasar nan ke ciki yasa suka shirya da takwaransa na Bauchi

- Kamar yadda Ortom ya sanar, yanzu ba lokaci bane na cacar baki tare da caccaka, lokaci ne na neman mafita

- A cewarsa, dukkansu gwamnoni ne kuma dole yasa su yi amfani da matsayinsu domin kare rayukan mutanensu

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana cewa sun yanke hukuncin yin sasanci shi da takwaransa na jihar Bauchi domin samun hanyar shawo kan lamurran da ke ci wa mutane kwarya a kasar nan.

Kafin nan, dukkan gwamnonin sun dinga tada kayar baya inda suke caccakar junansu a kan rikicin makiyaya da manoma, Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Ortom ya zargi Mohammed da bayyana goyon bayansa ga Fulani da ke yawo da makamai yayin da ya zargesa da zama cikin kungiyar 'yan ta'addan da ke addabar kasar nan.

KU KARANTA: Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom
Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Gwamnan da ya bayyana hakan a ranar Laraba a garin Makurdi jim kadan bayan ya dawo daga Fatakwal bayan takwaransa na jihar Ribas da Adamawa sun shirya su.

Kamar yadda Ortom yace, "Mun tattauna inda muka duba bukatar jam'iyyar da kuma kasar nan. Mun shirya domin mu samo hanyoyin shawo kan matsalar kasar nan.

"A don haka ne muka mayar da hankali wurin shawo kan matsalar tsaro ta kasar nan da ta ta'azzara. Dole ne mu hada kai da gwamnatin tarayya a wannan bangaren.

"A matsayinmu na gwamnoni, dole ne mu yi aiki a kungiyance domin tabbatar da tsaron mutanenmu."

KU KARANTA: Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada

A wani labari na daban, 'yan bindigan da suka sace 'yammatan makarantar Jangebe sun basu lambobin wayarsu bayan sakinsu da suka yi ranar Talata tare da yin alkawarin za su zo wurin iyayensu neman aurensu.

'Yanmatan da suka zanta da Daily Trust sun ce wadanda suka sace su sun sanar dasu cewa suna son su kuma sun yi alkwarin tuntubarsu ta waya domin jin ko sun samu karbuwa.

Wata daliba mai suna Hassatu Umar Anka, ta ce wadanda suka sace su sun basu shawarar su bar makaranta kawai su yi aurensu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel