Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya

Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya

- Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa ba zata bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta banza ba

- Gwamnatin jihar tace, kiwo sana'ar ta karan kai, dole ne makiyayan su zuba jarinsu a cikinta

- Gwamnan jihar ya bayyana wannan maganar ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba ta shafin Twitter

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba ya nanata cewa jihar ba za ta bayar da filaye kyauta don kiwo ba, yana mai cewa kiwo kasuwanci ne na kashin kai, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter yayin da yake karin bayani kan wani bayani da ya gabatar a baya game da shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a yayin taron tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.

“An ja hankalina zuwa ga batu game da aiwatar da Tsarin Canji na Kiwon Dabbobin Kasa yayin taron tsaro na hadin gwiwa, a jiya. Don guje wa shakku, lokacin da na ce za mu aiwatar da shirin, ba ina nufin aiwatar da tallata shirin bane," in ji Makinde a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Mai Tangale

Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya
Makinde: Ba za mu bada filayen kiwo ga makiyaya kyauta ba, dole su biya Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

“Zamu dauki bangarorin da suke da amfani ga jihar mu. Kamar yadda na sha fada a lokuta da dama, matsayinmu a Jihar Oyo shi ne, kiwon dabbobi kasuwanci ne na kashin kansa kuma ya kamata a gudanar dashi a haka.

"Gwamnatinmu ba zata samar da filaye kyauta ga masu saka jari masu zaman kansu ba.”

Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya kasance batun da aka dade ana yi a Najeriya. Ana zargin makiyayan da galibi ke kaura daga yankin arewacin kasar zuwa kudanci don neman wajen kiwo ana zargin wasu da aikata laifuka irin su satar mutane, fyade, da sauransu.

Amma makiyayan sun musanta aikata wani laifi, suna masu cewa ana siffanta su ba bisa ka'ida ba, an sace musu shanu da kuma lalata dukiyoyinsu.

A baya gwamnatin Najeriya ta tsara wasu matakai don dakile rikice-rikicen da ke faruwa wadanda suka hada da Ruga Crazing Area (RUGA), da kuma shirin sauya fasalin kiwo na kasa (NLTP). Sai dai, wadannan manufofin sun gamu da adawa mai tsauri.

Masu suka suna ikirarin cewa tsarukan na daga cikin wata makarkashiya da gwamnati ke yi na kwace filayen kakannin mutane, saboda tsoron cewa irin wannan yunkuri na iya haifar da mamayar kabilu.

KU KARANTA: APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Saraki

A wani labarin, Wasu manoman albasa da ‘yan kasuwarta a jihar Kano suna kukan kan tasirin katange kai kayan abinci zuwa yankin kudancin kasar nan.

Don nuna rashin amincewa da harin da aka kai wa ‘yan kasuwa a wasu Jihohin Kudu Maso Yamma, kungiyar Hadakar Dillalan Kayan Abinci da Shanu na Najeriya (AUFCDN) ta fara yajin aiki.

Wannan ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kudu amma a arewa, farashin na ta faduwa warwas.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel