APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Saraki

APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Saraki

- Tsohon kakain majalisar dattawa ta Najeriya ya siffanta APC da gazawa wajen gudanar da aiki

- Yace, bai kamata 'yan Najeriya su barwa APC kadai hakkin gyara matsalolin Najeriya ba a yanzu

- Ya kuma ce, ya kamata 'yan hamayya su ma su lalubo hanyar magance matsalolin kasar da kansu

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najariya Bukola Saraki ya ce, bai kamata a barwa jam'iyyar APC mai mulki matsalar Najeriya ba ita kadai ta shawo kansu ba, BBC Hausa ta rwaito.

Saraki wanda shi ne ke jan ragamar kwamitin sasantawa na jam'iyyar PDP, ya nuna cewa akwai bukatar hada hannu da 'yan hamayya domin lalubo mafitar da za a yi maganin matsalolin Najeriya baki daya, musammam a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Sarkin Tangale

APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Bukola Saraki
APC ba zata taba iya cire 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki ba, in ji Bukola Saraki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Saraki ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a dakin karatunsa na Abeokuta da ke jihar Ogun.

Tsohon shugaban Majalisar ya ce, "Idan muna maganar akan garkuwa da mutane, abin da ake bukata shi ne gwamnati da samar da shugabancin da zai kira wo duka masu ruwa da tsaki. mu zo a tattauna muga yadda za a shawo kan wannan matsaloli."

KU KARANTA: Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel