Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo

- Wata gobara da ba a san musabbabinta ba ta cinye wasu shaguna a kasuwar Sabo a jihar Oyo

- Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar ta harbu ne daga wani sashe na kasuwar zuwa wani

- An kashe gobarar, yayin da 'yan kasuwa ke kokawa kan irin tafka asara da suka yi dalilin gobarar

Wuta a tsakar dare ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo da ke garin Oyo, Jihar Oyo.

Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun shaida wa Premium Times cewa kayayyaki da dukiyoyi na biliyoyin nairori sun lalace yayin gobarar.

Gobarar, wacce aka ruwaito ta fara ne da misalin karfe 10:00 na dare, ta yadu zuwa mafi yawan sassan kasuwar ta Sabo.

Wasu 'yan kasuwa, wadanda shagunansu da kayayyakinsu masu dunbun daraja suka kone, an ce suna kukawa kan lissafa asarar da suka yi.

KU KARANTA: Da alamu gwamnatin Buhari bata fahimci matsalar tsaro a Zamfara ba, in ji gwamna Matawalle

Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo
Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar Sabo a jihar Oyo Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ba a iya gano musabbabin gobarar ba a lokacin hada wannan rahoton.

Wata majiya kuma ta shaida cewa jami’an kashe gobara sun isa wurin kuma ana ci gaba da kokarin kashe wutar.

Ba a iya samun Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Oyo, Adeleke Ismail ba har zuwa lokacin wannan rahoton saboda matsalar sadarwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, bai amsa kira da sakonnin waya ba shi ma.

KA KARANTA: Manoman albasa a jihar Kano sun fara shiga damuwa kan yajin aikin kai kaya Kudu

A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta bayar da rahoton wata gobara da ta barke a babban ofishinta da ke Abuja. An danganta abin da ya haddasa wutar da matsalar wutan r lantarki.

A cewar wata sanarwa daga Daraktan hulda da jama’a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima: “Matsalar wutar lantarki ne ya haifar da wata karamar gobara a Hedikwatar Sojoji dake Abuja da safiyar ranar Talata.

“Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 10:15 na safe ya kasance ne sakamakon karamar matsalar wutan lantarki a daya daga cikin ofisoshin."

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel