Daga nadin sabon shugaba, EFCC ta gurfanar da tsohon sanatan Kebbi a kotu
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wani sanatan jihar Kebbi a gaban kotu da zargin yin sama da fadi
- Wanda ake zargin bai bata wa kotu lokaci ba, ya amince da aikata laifin, yayin da aka nemi belinsa
- Kotu ta bada belin sanatan, ta kuma bada umarnin kwace fasfot din ketare mallakarsa har zuwa lokacin shari'a
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da Sanata Umaru Tafida-Argungu a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato kan tuhuma daya da ake yi masa na karkatar da kudin jama’a har N419,744,612.30.
A wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce tsohon sanatan wanda ya wakilci Kebbi ta Arewa a majalisar dattijai ya karkatar da adadin da gwamnatin jihar Sakkwato ta biya a matsayin 40% na hannun jari a Hijrah Investment Nigeria Limited.
Mista Uwujaren ya kara da cewa Gwamnatin jihar Sakkwato ta shiga yarjejeniya da tsohon Sanatan na sayen 40% na kamfaninsa Hijrah Investment Nigeria Limited domin samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Sai dai, bincike ya nuna an cire kudade da yawa daga asusun da aka ambata ga mutanen da ba su da alaka da manufofin juya kamfanin, Daily Nigerian ta ruwaito.
KU KARANTA: COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori
A ziyarar binciken da jami'ai suka yi wa kamfanin, ya nuna kamfanin na cikin mawuyacin halin ko in kula da mummunan lalacewa.
Tsohon sanatan bai ba kotu wahala ba, yayin da cikin sauki ya amsa tuhumar da ake masa.
Lauyan da ke gabatar da kara, S.H. Sa’ad ya roki kotu da ta fidda ranar da za a fara shari’ar yayin da lauyan da ke kare Ibrahim Abdullahi, ya gabatar da bukatar neman a ba shi belin wanda yake karewa.
Mai shari’a Mohammed ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 50 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Wadanda za su tsaya masa dole su kasance sun mika wani abinda suka mallaka na kadara ga ikon kotun. Alkalin ya kara yanke hukuncin cewa a ajiye fasfot din ketare kasa na wanda ake karan a kotun.
An daga karar zuwa ranar 18 ga Maris, 2021 don fara shari'a.
KU KARANTA: Matawalle: Zaku sha mamaki idan na tona asirin masu hannu a sace daliban Jangebe
A wani labarin, Majalisar dattijai ta fara tantance sabon Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, Vanguard ta ruwaito.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng