Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu

Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu

- Kungiyar ACF ta bukaci shugabannin kungiyar Hadin Kan Abinci da Dillalan Shanu da su janye takunkumin da suka sanya kan kudu

- Kungiyar dai tana yajin aikin kai kayan abinci da ake bukata daga arewa zuwa kudu kan rikicin Shaha

- ACF ta ce hakan bai da amfani domin ba yaki ake yi a Najeriya ba

Kungiyar dattawan Arewa (ACF), ta yi kira ga shugabannin kungiyar Hadin Kan Abinci da Dillalan Shanu da su janye takunkumin da suka sanya na kai kayan abinci daga arewa zuwa kudu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce: “Najeriya ba ta yaki da kanta kuma irin wannan tsattsauran mataki bai da amfani, amma zai kara dagula matsalolin tattalin arziki da siyasa da kasarmu ke fuskanta ne a yau.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Obasanjo, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun shiga labule yayinda tseren zaben 2023 ke kara zafi

Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu
Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

“Kungiyar ta ACF, ta damu da damuwar yan Najeriya dangane da shawarar da Hadaddiyar Kungiyar Abinci da dillalan shanu suka yanke na dakatar da zirga-zirgar abincin da ake bukata daga arewa zuwa kudu.

“Muna kira ga shugabannin kungiyar da su dakatar da abin da suke kira da takunkumi.

“Najeriya ba ta yaki da kanta kuma irin wannan tsattsauran mataki bai da amfani.

“Hakan zai kara dagula matsalolin zamantakewar tattalin arziki da siyasa da kasarmu ke fuskanta a yau.

“An ce mambobin kungiyar sun tafka asara mai yawa a lokacin tarzomar #Endsars da rikicin baya-bayan nan na Sasha a jihar Oyo da aka daidaici yan arewa.

“Mun yi imanin cewa koma wani irin matsaloli mambobinsu ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu a wasu sassan kasar, shugabannin ACF da nake jagoranta a shirye suke su taimaka masu wajen magance shi ta hanyar tattaunawa da hukumomin tsaro da na gwamnati.

“Babu bukatar wani yanki na kasar ya juya wa wani baya.

KU KARANTA KUMA: Bayan wata uku da sace su: Na ga mahaifina da yayata a wurin yan bindiga, dalibar Jangebe da aka sako

“Duk abin da zai iya zama bambance-bambancenmu, ACF a matsayinta na wacce ta yarda da cinikayyar yanci ta yarda cewa ya kamata a bar kayayyaki su yi zarya ckin walwala.

“Wannan matsanancin matakin ba ci gaba ba ne kuma bai da amfani. Wannan ba mafita bane."

A wani labarin, Kungiyar Arewa ACF, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki gwamnan jihar ta Zamfara, Bello Matawalle sannan su sa ya bayyana asalin wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe 317.

Kungiyar ta arewacin kasar ta bayyana cewa, idan har Gwamna Matawalle bai bayyana sunayen wadanda suka sace 'yan matan makarantar ba, ya kamata a dauki shi a matsayin wanda ke bada hadin kai wajen aikata laifin satar mutane.

An ruwaito Gwamna Matawalle ya fada wa Sarakuna 17 wadanda suka kai masa ziyarar jaje kan sace ’yan matan makaranta 317, cewa ya san wadanda suka sace su kuma idan ya bayyana asalinsu, ‘yan Najeriya za su firgita.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel