Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro

- Babagana Munguno ya shaida cewa, gwamnati nada rahotanni na wadanda ke cin ribar rashin tsaro

- Ya shawarci masu tada kayar baya da su maida hankalinsu wajen ganin sun wanzar da zaman lafiya

- Hakazalika ya gargadi masu tada zaune tsaye da su daina ko su fuskanci fushin gwamnatin tarayya

Babagana Monguno, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya ce wasu mutane suna amfani da damar tabarbarewar yanayin tsaro a kasar don amfanar kansu, TheCable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Talata bayan taron majalisar tsaron kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, Monguno ya ce gwamnati ba za ta lamunci lamarin ba.

Ya gargadi duk wadanda ke tayar da kayar baya da su daina ko kuma su samu kansu abin zargi.

“Tabbas, har yanzu shugaban kasa yana ci gaba da nuna damuwa game da matakin tsaro, wanda ake ganin yana neman zama mummunan aiki.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin soja

Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro
Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro Hoto: Information Guide Africa
Asali: UGC

"Ganin cewa muna da sabuwar kungiya tare da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro, shugaban kasa ya bukaci dukkanmu da mu rubanya kokarinmu, musamman ganin abubuwan da suka faru makonni biyu da suka gabata,” in ji Monguno.

“Yanzu, ina bukatar in kara jaddada cewa akwai wasu mutane a kasar nan wadanda suka dauki matsayin da ya wuce abin da ya kamata su zama.

"Bayanan da muke samu daga majiyarmu, bayanan da nake dasu da kuma na sauran bayanan sirri, sun nuna cewa muna da wasu kungiyoyi, wasu mutane da suke cin gajiya saboda rashin tsaro, musamman satar mutane."

Ya kuma gargadi wadanda ba ‘yan jiha ba da ke haifar da matsaloli a sassa daban-daban na kasar nan da su daina yin hakan, ya kara da cewa hukumomin leken asiri sun sanya musu ido.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Sarkin Kagara, garin da aka sace dalibai da malamansu ya rasu

A wani labarin, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya gargadi Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta tabbatar da cewa satar yaran makaranta bai sake faruwa ba, PM News ra ruwaito.

Atiku ya mayar da martani ne kan sakin 'yan mata 279 na makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, jihar Zamfara a ranar Talata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.