Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin soja

Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin soja

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin shugabannin rundunonin soja bayan bin diddigin rahoton Kwamitin Tsaro wanda ya bayar da shawarar tabbatar da su, The Nation ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Laraba da ta gabata ya mika bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na tabbatar da sabbin hafsoshin tsaron, ga kwamitin tsaro.

Lawan ya bai wa kwamitin karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko makonni biyu don gudanar da ayyukansu tare da gabatar da rahoto ga majalisar dattijai a zama na gaba.

Karin bayani nan gaba...

Asali: Legit.ng

Online view pixel