Buhari, Osinbajo da sauran fitattun Najeriya za su yi rigakafin COVID-19 ranar Asabar

Buhari, Osinbajo da sauran fitattun Najeriya za su yi rigakafin COVID-19 ranar Asabar

- Ana sa ran isowar allurar rigakafin Korona a yau Talata 2 ga watan Maris a babban birnin tarayya

- Shugaba Muhammadu Buhari da makusantansa a fannin mulki su ne zasu kasance na farkon yin rigakafin

- Kafin a fara yin allurar, an bayyana tura ta ga hukumar NAFDAC don aiwatar da cikakken bincike

Shugaba Muhammadu Buhari, Mataimakinsa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha da sauran fitattun ‘yan Najeriya za su kasance cikin sahun farko na 'yan Najeriya da zasu yi allurar rigakafin COVID-19 ta gidan talabijin kai tsaye.

Ana sa ran za su fara allurar ta farko a ranar Asabar, 6 ga Maris.

Babban Darakta/Shugaba, na Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaib, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron hadin gwiwa na kasa da aka yi na Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan COVID-19.

Daily Trust ta ruwaito cewa allurai miliyan hudu na allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca COVID-19 za su iso kasar daga Indiya yau Talata.

Shuaib ya ce, a ranar 6 ga watan Maris, Shugaba Buhari, Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo, SGF da sauran fitattun ‘yan Nijeriya za su kasance cikin sahun farko na 'yan Nijeriya da za su yi allurar.

KU KARANTA: Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5

Buhari, Osinbajo da sauran fitattun Najeriya za su yi rigakafin Korona ranar Asabar
Buhari, Osinbajo da sauran fitattun Najeriya za su yi rigakafin Korona ranar Asabar Hoto: Business Day
Source: UGC

A cewarsa, wannan zai taimaka wajen wayar da kan mutane game da kwayar cutar da kuma allurar rigakafi a kasar idan ta iso.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa kan allurar rigakafin idan ta iso Najeriya.

A bayanin da ya gabatar ranar Litinin, Faisal ya ce kashin farko na allurar rigakafin Oxford/AstraZeneca COVID-19, wanda ya kai kimanin allurai 3,924,000, ana sa ran zai iso Najeriya yau Talata, 2 ga Maris 2021 da karfe 11:10 na safe.

Ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa an tsara duk matakan da suka dace na kiyaye lafiya da ingancin shigowarta, adanata da kuma nasarar gudanar da rigakafin a kasar.

A cewarsa, za a yi wani karamin biki wanda shugaban PTF a kan COVID-19 zai jagoranta don karbar allurar a sashen VIP Protocol, a babban filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe International dake Abuja.

Ya ce a karshen bikin, domin nuna alamar isowar allurar rigakafin, za a mika wasu kadan daga cikin allurar rigakafin ga hukumar NAFDAC wadanda za su yi nazari a kai na tsawon kwanaki biyu (Laraba, 3 ga Maris da Alhamis, 4 ga Maris) ).

KU KARANTA: Daga nadin sabon shugaba, EFCC ta gurfanar da tsohon sanatan Kebbi a kotu

“Bugu da kari kan yardar NAFDAC, PTF, FMOH, NPHCDA da shugabannin dabaru, za su kasance a cibiyar kula na Asibitin Tarayya a ranar Juma’a, 5 ga Maris 5 2021, inda za a kafa wurin yin allurar rigakafin farko don fara rigakafin ga ma’aikatan lafiya da ma’aikatan tallafi.

"Wadannan Ma’aikatan suma za a yi musu rajista ta yanar gizo a cikin ma’adanar rigakafin COVID-19 kuma za su karbi katin rigakafinsu na COVID-19 wanda ke da lambar QR da za a iya tabbatar da shi a duk duniya.

"A ranar Asabar, 6 ga Maris, manyan shugabannin dabarun za su yi allurar farko na rigakafin," in ji Faisal.

A wani labarin, Farfesan ilimin kwayar cuta, Oyewale Tomori, ya ce kamata ya yi jami’an gwamnati su kasance cikin wadanda za su fara yiwa allurar rigakafin COVID-19 lokacin da ta iso Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Tomori ya ce irin wannan matakin zai gamsar da 'yan Najeriya game da lafiyar alluran rigakafin da ake sa ran isowarsu ranar Litinin. Ya fadi haka ne a lokacin da ake zantawa da shi a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel