Da dumi-dumi: An sako daliban GGSS Jangebe 317 dake jihar Zamfara

Da dumi-dumi: An sako daliban GGSS Jangebe 317 dake jihar Zamfara

‘Yan mata 317 da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun dawo, in ji Gwamnan Jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita cikin daren Talata, 2 ga Maris, 2021.

A jawabinsa, ya bayyana irin jajircewan da suka yi domin ganin cewa an sako wadannan dalibai 317.

“Alhamdulillah! Ina matukar farin ciki da sanar da sakin daliban GGSS Jangebe da aka sace daga masu garkuwa da mutane.

"Wannan ya biyo bayan fadada jajircewa da yawa da aka sanya akan kokarin mu. Ina yi wa dukkan 'yan Najeriya masu kyakkyawar niyya murna da mu saboda 'ya'yanmu mata yanzu sun dawo cikin lafiya," Matawalle ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel