COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

- Wani jami'i a Najeriya ya kirayi gwamnati da ta fara yiwa jami'anta rigakafin Korona kafin talakawa

- Ya bukaci da bayan an yi musu basu mutu ba, to kowa zai yarda a yi masa ba tare da musu ba

- Hakazalika yace, shugabanci ya kamata ya kasance daga sama zuwa kasa a kasar ta Najeriya

Farfesan ilimin kwayar cuta, Oyewale Tomori, ya ce kamata ya yi jami’an gwamnati su kasance cikin wadanda za su fara yiwa allurar rigakafin COVID-19 lokacin da ta iso Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Tomori ya ce irin wannan matakin zai gamsar da 'yan Najeriya game da lafiyar alluran rigakafin da ake sa ran isowarsu ranar Litinin.

Ya fadi haka ne a lokacin da ake zantawa da shi a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin.

KU KARANTA: Ba batun caccakar gwamnati bane yasa DSS ta kame Yakasai, PRO

Don gamsar da 'yan Najeriya, ya kamata a fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin COVID-19 Tamori
Don gamsar da 'yan Najeriya, ya kamata a fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin COVID-19 Tamori Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

"Ya kamata mu ga wasu daga cikin wadancan jami'an gwamnatin sun fara yin alluran rigakafi sannan sai mu lura da su mu ga ko sun tsira ko ba su tsira ba. Sannan a hankali, sai mu fara gina rigakafin mutane,” inji shi.

“Amma ka ce min na je nayi allurar sannan kana kai yaranka Dubai don ka suje su yi wani rigakafin, tabbas, ba zan yarda da kai ba.

“A yi shi a fili a dandalin Eagles Square. A samu manyan mutane a wurin, 'yan majalisar dokoki, kowa, to za mu shawo kan mutanenmu cewa babu matsala a dauke su (rigakafin)."

Tomori ya ce da zarar an yiwa shugabannin rigakafi, mutane za su fara samun kwarin gwiwa a kan alluran.

“Abu ne sannu a hankali, bayan lokaci mutane yanzu zasu fara cewa wadannan mutane da suka yi basu mutu ba, basu yi rashin lafiya ba, saboda haka, zan iya zuwa nima na yi. Abin da ya kamata mu yi ke nan. Shugabanci a kasar nan dole ne ya zo daga sama,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Baya ga ma’aikatan lafiya, ya kamata mu sa shugabanninmu su fito can a fili su yi wannan allurar. Zan kasance daya daga cikin wadanda za su je can su yi allurar. ”

KU KARANTA: Sunday Igboho: Sai na kafa Jamhuriyar Oduduwa, kuma zan kashe Yarbawa masu hana ni kafin 2023

A wani labarin, Ministan lafiya Osagie Ehanire ya fada a Lagas jiya cewa Najeriya na iya samun allurar rigakafin COVID-19 nan da kwanaki 10 masu zuwa, The Nation ta ruwaito.

Ministan ya ce "An gaya mana cewa a karshen wannan watan, wato kimanin kwanaki 10 kenan daga yanzu, za mu sami alluran." “Ba mu kera alluran ba.

Ana kera su ne a kasashen waje a cikin kasashe kamar hudu ko biyar," kamar ydda ya fada wa manema labarai a karshen ziyarar rangadin asibitin koyarwa na jami'ar Legas (LUTH), Idi-Araba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.