Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dandalin rajistar rigakafin Korona ta yanar gizo

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dandalin rajistar rigakafin Korona ta yanar gizo

- A jiran isowar allurar rigakafin Korona Najeriya, gwamnati ta kaddamar da hanyar rajistar yin allurar

- Gwamnatin ta kaddamar da wata kafar yanar gizo domin yin rajistar allurar cikin sauki

- Hakazalika, an gayyaci 'yan Najeriya da su hanzarta zuwa kafar domin rajistar yin allurar

A ci gaba da shirye-shiryen tabbatar da tsaron lafiyar 'yan Najeriya da kuma yaki da annobar kwayar cutar COVID-19, gwamnatin Najeriya na tsammanin isowar allurar rigakafin da ta saya watanni kadan da suka gabata.

Hakazalika, Najeriya ta kaddamar da kafar yanar gizo don rajistar rigakafin COVID-19 yayin da kasar ke jiran isowar allurai miliyan hudu na AstraZeneca COVID-19 ranar Talata.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko ta kasa zata hanzarta fara yiwa 'yan Najeriya rigakafin a manyan kungiyoyi, inda zata fara da manyan ma'aikatan lafiya.

KU KARANTA: Matawalle: Zaku sha mamaki idan na tona asirin masu hannu a sace daliban Jangebe

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dandalin rajistar rigakafin Korona ta yanar gizo
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dandalin rajistar rigakafin Korona ta yanar gizo Hoto: @NphcdaNG.
Asali: Twitter

A ruwayar The Guardian, shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Firamare ta Kasa, Faisal Shuaib yace:

"Mun samar da hanyar yin rajista ta yanar gizo domin baiwa 'yan Najeriya damar yin rajistar allurar COVID19 da kansu, samun lambobin rigakafin su da kuma tsara lokutan da suka fi so domin yin rigakafin," in ji shi

Karshe an gayyaci ‘yan Nijeriya da su yi rajista ta yanar gizo na NPHCDA domin rigakafin COVID-19.

Dangane da wadanda basu da damar yin rajistar ta yanar gizo, Shuaib yace za a basu "damar yin rajistar gida-gida don sanya su a cikin rumbun adana bayanai don yin allurar rigakafi ta amfani da tsarin T.E.A.C.H."

Ku yi rajista ta nan: www.nphcdaict.com.ng/publicreg/

KU KARANTA: Amurka ta sayarwa Najeriya jiragen yaki guda 12 kirar A-29 Super Tucano don yakar 'yan ta'adda

A wani labarin, Farfesan ilimin kwayar cuta, Oyewale Tomori, ya ce kamata ya yi jami’an gwamnati su kasance cikin wadanda za su fara yiwa allurar rigakafin COVID-19 lokacin da ta iso Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Tomori ya ce irin wannan matakin zai gamsar da 'yan Najeriya game da lafiyar alluran rigakafin da ake sa ran isowarsu ranar Litinin. Ya fadi haka ne a lokacin da ake zantawa da shi a shirin Sunrise Daily na Channels Television a ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel