Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna

Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna

- Wasu bata gari da ake zargin 'yan bindiga ne sun halaka mutane guda bakwai a wasu garuruwan jihar Kaduna

- Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi

- Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun rahoton ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasu ta'aziyya

Gwamnatin Jihar Kaduna a ranar Lahadi ta ce yan bindiga sun halaka mutane bakwai a sassa daban-daban a jihar, rahoton PM News.

Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna.

Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna
Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An sace mutum 7 yayin da yan bindiga suka kai hari wani makaranta a Kagara

Aruwan ya ce, "Cikin bakin ciki, jami'an tsaro sun bada rahoton cewa yan bindiga sun kai wa wasu mutane hari a kauyen Kajinjiri da ke karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane biyu."

Ya ce wani mutum daya ya samu raunuka sakamakon harbinsa da bindiga da suka yi kuma ana jinyarsa a wani asibiti.

"Kazalika, a kauyen Rago da ke karamar hukumar Igabi, yan bindiga sun kashe mutanen garin biyu," in ji shi.

Ya yi bayanin cewa a wani harin daban, yan bindiga sun kai hari Kutura Station, Karamar hukumar Kajuru, sun kashe mazauna garin uku.

KU KARANTA: Za ka ɗaukaka a siyasa: Martanin tsohon gwamnan PDP kan tuɓe Ɗawisu da Ganduje ya yi

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun rahoton ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasu ta'aziyya tare da addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Ya kuma yi wadanda suka jikkata sakamakon harin Kajinjiri fatan samun sauki cikin gaggawa.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164