Za ka ɗaukaka a siyasa: Martanin tsohon gwamnan PDP kan tuɓe Ɗawisu da Ganduje ya yi

Za ka ɗaukaka a siyasa: Martanin tsohon gwamnan PDP kan tuɓe Ɗawisu da Ganduje ya yi

- Jigo a PDP, tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya jinjinawa tuɓaɓen hadimin Ganduje, Salihu Tanko Yakasai

- Bayan jinjina wa Ɗawisun, Fayose ya ce ya zama jarumin demokradiyya kuma tube shi zai dama dalilin ɗaukakarsa a siyasa

- Fayose ya kuma bayyana matakin da Ɗawisu ya ɗauka na faɗa wa gwamnati gaskiya a matsayin dattaku

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yabawa Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da aka sallama saboda sukar Buhari a shafinsa na Twitter.

Fayose ya yi wannan jinjinan ne bayan Alhaji Tanko Yakasai, mahaifin Salihu Tanko Yakasai ya bada rahoton cewa jami'an tsaro sun kama dansa saboda ya ce Shugaba Buhari ya yi murabus yayin Allah wadai da sace ɗaliban GGSS Jangebe a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami hadiminsa Salihu Tanko Yakasai, Dawisu

Dawisu: Za ka samu ɗaukaka a siyasa, tsohon gwamnan PDP ya yi martani kan tuɓe hadimin Ganduje
Dawisu: Za ka samu ɗaukaka a siyasa, tsohon gwamnan PDP ya yi martani kan tuɓe hadimin Ganduje. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

Amma, Fayose ya ce matakin da Yakasai ya ɗauka ya maida shi jarumin demokradiyya kuma alama ce da ke nuna haɗin kan Nigeria.

A cewarsa, tuɓe shi daga mukaminsa ne farkon samun daukakarsa a siyasa.

Tsohon gwamnan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Na yaba wa jarumtar Salihu Yakasai, tuɓaɓen hadimin Gwamna Ganduje saboda ya faɗa wa masu mulki gaskiya.

"Wannan abinda da ya yi kawai ya mayar da shi jarumin demokradiyyar mu a Nigeria kuma hakan ma nufin muna fatan Nigeria za ta cigaba da ɗorawa a matsayin ƙasa ɗaya.

KU KARANTA: Bidiyon wani yana rushe gidan da ya gina wa budurwarsa saboda ta ce bata son shi

"Babu abinda ya fi dattaku fiye da fadin gaskiya a lokacin mulki na son kai. Korarsa shine farkon ɗaukakarsa a siyasa.

"Ina taya shi murna da sauran ƴan Nigeria da ke neman ganin an samu shugabanci da mulki nagari."

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel