Yanzu-yanzu: An sace mutum 7 yayin da yan bindiga suka kai hari wani makaranta a Kagara
Yan bindiga sun kai hari Government Technical College, Kagara da ke karamar hukumar Rafi na jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.
Majiyoyi sun bayyana wa Daily Trust cewa yan bindigan sun afka makarantar ne daren jiya amma ba su tarar da kowa ba.
Gwamnati ta rufe sukkan makarantun da ke garin bayan sace dalibai da ma'aikatan GSS Kagara.
Yan bindigan da suke nufin sace mutane da yawa sun bar makarantar cikin fushi suka tafi wani gari da ke kusa da makarantar suka sace mutum bakwai.
DUBA WANNAN: Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano
A cewar majiyar wadanda aka sace sun hada da Alhaji Aminu, mai kamfanin ruwa na Kongwama.
Lamarin ya faru ne bayan sakin daliban makaranatar Kwallejin kimiyya na gwamnati da ke Kagara.
Bayan sakin yan makarantar, yan bindiga sun kai hare hare a wasu kauyuka da ke kagara inda suka halaka mutane hudu.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Masu garkuwa sun sako 'yan matan makarantar Zamfara
Sun sace mutane 11 cikinsu har da mata bakwai yayin da suka sace shanu.
A ranar Juma'a, shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi yan bindigan inda ya ce ba su fi karfin gwamnatinsa ba.
Buhari ya ce ba domin gudun salwantar da rayyukan wadanda yan bindigan ke garkuwa da su ba da tuni sojoji sun gama da su.
Shugaban kasa ya kuma shawarci gwamnoni su dena biyan yan bindiga kudin fansa.
A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.
A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng