Pantami da NSA sun sha banban kan batun ƙaddamar da fasahar 5G a Nigeria

Pantami da NSA sun sha banban kan batun ƙaddamar da fasahar 5G a Nigeria

- Ministan Sadarwar Nigeria, Dr. Ali Pantami da ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, NSA, sun sha banban kan fasahar 5G

- A yayin da Pantami ke ganin ana iya kaddamar da fashar a Nigeria nan bada dadewa ba, ofishin na NSA na nuna damuwa kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar

- Pantami ya bada tabbacin cewa an yi gwajin 5G a Nigeria da kasashen waje kuma ba a samu wani matsala ba don haka ana iya kaddamar da fasahar

Ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

DUBA WANNAN: Ba zan yi wa ƴan bindiga afuwa ba, in ji Shugaba Buhari

Pantami da NSA sun sha banban kan kaddamar fasahar 5G a Nigeria
Pantami da NSA sun sha banban kan kaddamar fasahar 5G a Nigeria. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Kakakin ofishin NSA, Bala Fakandu ya ce suna da damuwa kan matsalolin da ke tattare da fasahar ta 5G kamar yiwuwar leken asirin kasa, harin yanar gizo, leken asirin sojoji da wasu ababe da kasashen waje ka iya yi don haka ta yi kira da ofishin Pantami su sake yin nazari kan fasahar domin tabbatar da cewa ba za a fuskanci matsala ba.

A bangarensa, Pantami ya ce ma'aikatarsa ta yi gwajin farko kan fasahar ta 5G a ranar 25 ga watan Satumbar 2019 kuma tana daf da tattara rahoton ta na karshe.

KA KARANTA: Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa

"Mafi yawancin abinda muka cimma zai kasance cikin rahoto na da zan gabatar wa FEC.

"Matsayin shine mun kusa kaiwa matakin karshe. Don haka, Najeriya na iya kaddamar da 5G da zarar mun magance manyan kallubalen," in ji shi.

Ya ce kawo yanzu babu wasu matsaloli da aka samu a binciken da aka gudanar a kasahen ketare da aka yi gwajin a gida da kasashen waje.

Ya bada tabbacin cewa 5G bata da alaka da annobar coronavirus ko wata cutar.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce majalisar zata amince da 5G din ne idan an tabbatar ba zata shafi lafiya da tsaron yan Najeriya ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel