Yanzu-yanzu: Masu garkuwa sun sako 'yan matan makarantar Zamfara

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa sun sako 'yan matan makarantar Zamfara

- An sako yan matan makarantar karamar sakandare ta gwamnati da ke Jangebe a jihar Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da sakin daliban da aka sace su daga makarantarsu a ranar Juma'a

- A halin yanzu yan matan suna fada mai martaba sarkin Anka inda daga nan za a tafi da su Gusau, babban birnin jihar Zamfara

Rahotannin da muka samu daga The Punch na cewa an sako yan matan makarantar Government Secondary School, Jangebe, da ke jihar Zamfara.

A halin yanzu suna fadar mai martaba sakrkin Anka suna jirar motar da zai kai su Gusau babban birnin jihar.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sake komawa Kagara, sun bindige mutum hudu har lahira

Yanzu-yanzu: Masu garkuwa sun sako 'yan matan makarantar Zamfara
Yanzu-yanzu: Masu garkuwa sun sako 'yan matan makarantar Zamfara. @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da sakin ƴan matan amma a yanzu ba a tantance adadin waɗanda aka sako ba.

Ana kyautata zaton ƴan bindigan sun tafi da ƴan matan daji ne bayan sace su a ranar Juma'a.

Majiyoyi sun bayyana cewa an ajiye matan a wani daji da ke tsakanin Dangulbi da Sabon Birnin a ƙaramar hukumar Maru, Zamfara.

KU KARANTA: Harin Jangebe: Ganduje ya bada umurnin rufe makarantun kwana 10 a Kano

Wannan shine satan ɗalibai na baya-baya da ƴan bindigan suka yi a Arewa cikin yan makonnin nan.

A makon da ya gabata, yan bindiga sun sace ɗalibai da ma'aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar Neja.

Gwamnatin jihar Neja ta ce ba ta biya kudin fansa ba kafin aka sako daliban da malaman.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164