Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne

Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne

- Wani tsohon daraktan DSS ya bayyana cewa da yawan 'yan bindiga tsoffin 'yan Boko Haram ne

- Daraktan yace babu hadi tsakanin aikata manyan laifin 'yan Neja Delta da na 'yan bindiga

- Ya kuma bayyana cewa wasu kam ma bakine daga kasashen ketare dake son zama don lalata kasar

Dennis Amachree, wani tsohon mataimakin darakta a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ya ce wasu ‘yan bindiga tsoffin mambobin kungiyar Boko Haram ne, TheCable ta ruwaito.

Da yake magana lokacin da yake gabatarwa a wani shirin Arise TV a ranar Asabar, Amachree ya ce ya fahimci hakane daga ikirarin da wasu 'yan bindiga suka yi.

Ya kara da cewa ba kamar tsagerun Neja Delta da ke zanga-zangar gurbacewar yankunansu ba, 'yan bindiga ba su cancanci a yi musu afuwa ba domin su "masu laifi ne marasa alkibla"

"Bisa ga bincike, mun gano cewa wasu daga cikinsu mayakan Boko Haram ne," in ji shi.

“Wasu daga cikinsu sun yi ikirarin sun yi fada da Boko Haram. Yanzu kuma, kuna da wadannan mutanen suna kutsawa, suna karbar kudin fansa, suna yiwa mata fyade tare da mayar dasu kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: Daliban Kagara: Wadanda suka sace mu kullum lakada mana duka suke, su ciyar damu wake

Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne
Tsohon Daraktan DSS: Da yawan 'yan bindiga tsofaffin 'yan Boko Haram ne Hoto: Aris Tv
Asali: UGC

“Duk wanda yake kwatanta su da tsagerun Neja Delta, ina son mutumin ya fada min menene manufar su. Ba za ku iya zama a matsayinku na kasar da ke ma'amala da masu aikata laifuka marasa manufa ba, wadanda ke muzgunawa al'ummarku, kuma ku sake su haka siddan.

“Abin da ya faru a yankin Neja Delta ya sha bamban da abin da muke fuskanta a yanzu."

"A yankin Neja Delta, mutane sun yi zanga-zanga ne saboda gurbata muhallansu. Kuma saboda haka, suka ce ‘idan kuna dibar mai kuma ba za mu ci gajiyar sa ba’, to daga nan suka fara fashe wuraren shigar da mai.”

Amachree ya kara da cewa yayin da aka san shugabannin 'yan bindiga, wasu daga cikin 'yan bindigar 'yan kasashen waje ne da ke son yin rayuwarsu ta kashin kai a Najeriya.

“Ga wadannan 'yan bindigan, muna magana ne game da 'yan ta'adda, wasu da muka gano ba ‘yan Nijeriya bane.

"Don haka, suna shigowa wannan kasar, suna mamaye wuraren da ba mu da mulki kuma suna kokarin zama a can karkashin ka'idojinsu. Don haka, wadannan 'yan bindigan barayi ne,” ya kara da cewa.

KU KARANTA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

A wani labarin, Dalibai da sauran wadanda aka suka sace daga GSC Kagara a Jihar Neja an sake su a safiyar ranar Asabar bayan amincewar jami'ai su saki mambobin 'yan bindigan su hudu, kamar yadda majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa Daily Trust ranar Lahadi.

Kungiyar 'yan bindigar sun kai hari a makarantar da ke cikin Karamar Hukumar Rafi a ranar 17 ga Fabrairu inda suka yi awon gaba da dalibai 27, da malamai 3, da ma'aikata 2 da ba sa koyarwa da iyalansu mutum 9.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel