Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga

Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga

- Shararren marubuci Wole Soyinka ya shawarci jihohi da su shiga zanga-zanga kan sace yara

- Ya nemi jihohin da abin ya shafa da makwabta da su gaggauta tsundumawa zanga-zanga

- Hakazalika ya kalubalanci gwamoni da su gaggauta daukar mataki ba wai su miki kafa ba

Shararren marubuci Farfesa Wole Soyinka, a ranar Asabar ya ce daga yanzu, duk jihar da ake satar yara ya kamata ta rufe don nuna rashin amincewa da ta'addancin, The Punch ta ruwaito.

Soyinka ya kuma shawarci sauran jihohin da ke makwabtaka, a matsayin hadin kai, su ma su shiga zanga-zangar tare da rufe jihohinsu.

Marubucin ya yi magana ne jim kadan bayan laccar da ya gabatar na sabon littafinsa, ‘Chronicles of the happiest people on Earth,' a Abeokuta, Jihar Ogun. Kungiyar Marubutan Najeriya, reshen jihar Ogun ne suka shirya shirin tare da hadin gwiwar kungiyar Abeokuta Club.

Fiye da ‘yan mata 300 'yan makaranta aka sace a ranar Juma’a a Zamfara, wanda shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin wadannan hare-hare, yayin da aka kuma sace dalibai 27 a Kangara, Jihar Neja, amma an sake su bayan sama da mako guda.

KU KARANTA: Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga
Soyinka: Ya kamata duk jihar da ake sace yara su tsunduma zanga-zanga Hoto: This Day News
Asali: UGC

Marubucin wanda ya koka kan yadda gwamnati da hukumomin tsaro suka kunyata 'yan Najeriya, ya ce bai san wani abin da za a ba da shawara a matsayin magani ga "lokutan firgici ba"

Soyinka ya kara da cewa irin wannan satar ba abu ne da za a lamunta ba kuma dole ne a dauki “tsauraran matakai masu ma’ana” a kai.

Ya ce, “Ina ganin mun kai matsayin da, a kowace jiha, inda aka sace kowane yaro, ya kamata wannan jihar ta garkame gaba daya.

"Kuma sauran jihohi, cikin hadin kai, ya kamata su duba rufe wasu ayyukansu. Hakan nada wahala amma, ba mu san abin da wani zai iya ba da shawara a wannan lokacin na musamman ba. Eh, rayuwa dole ne ta ci gaba amma wadannan ayyukan za su haifar da habaka rayuwarmu.

Soyinka ya kara da cewa, “ba za mu iya ci gaba da wannan salon ba. Wani abu mai mahimmanci, mai ma'ana dole ne ya faru, kuma ya zama gama gari.

KU KARANTA: Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38

A wani labarin, Dalibai, malamai da danginsu na Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, jihar Neja da 'yan bindiga suka sace kwanaki 11 da suka gabata sun sun kubuta da sanyin safiyar jiya tare da labarin azabtarwa da wulakanci.

Amma suna farin ciki da cewa suna raye don bayar da labarai, ko da yake daya daga cikin daliban an garzaya da shi asibiti saboda abinda Gwamna Abubakar Sani Bello ya kira gajiyar da ta wuce kima.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel