Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana

- Kungiyar dattawan Arewa sun bayyana jimaminsu na yawaita satan yaran makaranta a arewa

- Kungiyar ta roki iyaye da kada su bari rikicin satan ya sa su yanke shawarin cire yaransu a makaranta

- Hakazalika sun shawarci gwamnonin jihohi da su bullo da hanyar da zasu magance matsalar tsaro a jihohinsu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a jiya ta yi kira ga iyayen da ke da ’ya’ya a makarantun kwana a yankin arewa cewa kada su karaya game da yawan sace-sacen mutane ba kakkautawa a jihohin Zamfara da Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar, ta bakin Daraktan Yada Labarai da Bayar da Shawara, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya kuma nuna kaduwa da haushi game da yawaitar sace-sacen yara ‘yan makarantar kwana a sassa daban-daban na Arewa.

KU KARANTA: Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo ba, haka aka sako 'yan GSC Kagara

Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana
Dattawan Arewa ga 'yan Arewa: Dan Allah kada ku debe 'ya'yan ku a makarantun kwana Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Kungiyar, yayin kokawa game da karuwar hatsari ga rayuwar ‘yan Najeriya duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar cewa za ta kawo karshen 'yan bindiga da sace-sacen mutane, ta bukaci iyaye da su bijire wa firgicin cire 'ya’yansu daga makarantu.

Dattawan sun shawarci gwamnoni da su binciki al'amuran da ke haifar da yaduwar ta'addancin a matakin kananan hukumomi da na al'umma tare da warware su, suna masu cewa 'yan kasa su shirya tare da kara kaimi wajen taka tsantsan.

Baba-Ahmed ya jaddada cewa ya kamata gwamnoni su tunkari matsalar ta hanyar amfani da wata hanyar daban, yana mai cewa duk wani dan bindiga da ba ya shirye don zaman lafiya kamar yadda wasu gwamnoni suka fara ya kamata a bi shi yadda ya kamata.

KU KARANTA: Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38

A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce duk da tabbaci daga gwamnatin tarayya cewa za ta kawo karshen ‘yan bindiga da sace-sacen mutane; rayukan 'yan Najeriya na kara shiga cikin hadari, The Cable ta ruwaito.

Taron na mayar da martani ne kan batun sace-sacen mutane, musamman sace 'yan makaranta mata 317 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe a karamar hukumar Talata-Mafara, a jihar Zamfara.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel