Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38

Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38

- Gwamnati ta saki wasu 'yan bindiga hudu kafin a sako daliban GSC Kagara da malamansu

- Majiya mai karfi ta tabbatar da hakan, yayin da gwamnatin jihar ta karyata biyan fansa

- Gwamnatin jihar ta bayyana kokari da dabarunta wajen ganin an sako daliban da malamansu

Dalibai da sauran wadanda aka suka sace daga GSC Kagara a Jihar Neja an sake su a safiyar ranar Asabar bayan amincewar jami'ai su saki mambobin 'yan bindigan su hudu, kamar yadda majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin suka shaida wa Daily Trust ranar Lahadi.

Kungiyar 'yan bindigar sun kai hari a makarantar da ke cikin Karamar Hukumar Rafi a ranar 17 ga Fabrairu inda suka yi awon gaba da dalibai 27, da malamai 3, da ma'aikata 2 da ba sa koyarwa da iyalansu mutum 9.

Bayan kwanaki ana aiki don tuntubar wadanda suka sace su da kuma tattaunawar da ta biyo baya, an sake wadanda aka sacen ga hukumar ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da misalin karfe 7 na safiyar Asabar.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara

Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38
Kasurgurman 'yan bindiga 4 gwamnati ta saki a matsayin fansan daliban Kagara 38 Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Wadanda aka sacen da Gwamna Abubakar Sani Bello ya tarbe su a ranar Asabar sun ba da labarin irin mummunan halin da suka shiga a hannun wadanda suka sace su.

Daily Trust a ranar Lahadin da ta gabata ta samo daga majiya mai tushe cewa masu garkuwar, wadanda ke barna tsakanin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, da Rafi a Jihar Neja, sun bukaci a saki mambobin kungiyar su shida da jami’an tsaro suka kama a lokuta daban-daban.

Hudu daga cikin mutane shida da suke bukata a saka, an gano su a wuraren tsarewa daban-daban a jihohin Katsina, Kaduna da Neja.

Gwamnatin jihar Neja ta shaidawa manema labarai a jiya cewa ba a biya kudin fansa ba don sakin mutanen da abin ya shafa. Kwamishinan yada labarai, Alhaji Muhammad Sani Idris, ya ce babu musayar fursunoni kawai an amfani da dabarun gwamnati ne wajen sakin daliban.

Amma wata majiya ta shaida a ranar Lahadi cewa an saki biyu daga cikin mutanen da aka gano ga 'yan bindigan kafin a sako daliban.

Majiyar ta bayyana cewa, “an kammala shirin da za a saki sauran biyun,” in ji majiyar.

A ranar Lahadin da ta gabata ta gano cewa ’yan bindigan sun sa wadanda lamarin ya rutsa da su cikin dazuzzuka, lamarin da ya sa ya zama da wuya a same su cikin sauki.

“Daya daga cikin 'yan bindigan da aka yi amfani da su wajen isa ga kungiyar ya hau babur na tsawon awanni tara domin ya je ya hadu da Kachalla (shugaban) masu garkuwar.

"An shawo kan Kachalla don ya ba da damar a saki wadanda aka sacen duk da cewa ba duk mutanen da suke so ba ne aka sakar musu.

“Tsakanin inda shugaban yake da wurin da suka boye wadanda lamarin ya shafa wata tafiya ce mai nisa. Don haka ya kasance mawuyacin hali kuma fiye da yadda wadanda aka sace din zasu iya takawa na tsawon awanni masu yawa zuwa kubutarsu.” in ji majiyar.

A halin yanzu, rana ce ta juyayi ga wadanda abin ya shafa da iyayensu, yayin da wadanda aka sacen suke ba da labarin halin da suka shiga yayin ganawarsu da Gwamna Abubakar Sani Bello a gidan gwamnati dake Minna.

KU KARANTA: Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

A wani labarin, Abubakar Bello, gwamnan Neja, ya ce jiharsa ba ta biya fansa ba don sakin dalibai da malamansu da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, TheCable ta ruwaito.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, ‘yan bindiga sun far wa makarantar GSC Kagara kuma suka yi awon gaba da dalibai, ma’aikata, da danginsu. Wadanda aka sacen da aka saka a ranar Asabar, an tarbe su ne a gidan gwamnatin jihar dake Minna, babban birnin jihar Neja.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel