Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo ba, haka aka sako 'yan GSC Kagara

Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo ba, haka aka sako 'yan GSC Kagara

- Gwamnan Neja ya tabbatar da cewa gwamnatinsa bata biya kudin fansa don sakin dalibai ba

- Gwamnan jihar, ya siffanta aikin ceton daliban da malamansu da aikin mai matukar wahala

- Ya kuma godewa masu ruwa da tsaki da suka tallafa wajen ganin an cimma nasarar sakinsu

Abubakar Bello, gwamnan Neja, ya ce jiharsa ba ta biya fansa ba don sakin dalibai da malamansu da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati dake Kagara, TheCable ta ruwaito.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, ‘yan bindiga sun far wa makarantar GSC Kagara kuma suka yi awon gaba da dalibai, ma’aikata, da danginsu.

Wadanda aka sacen da aka saka a ranar Asabar, an tarbe su ne a gidan gwamnatin jihar dake Minna, babban birnin jihar Neja.

KU KARANTA: Dattawan Arewa: Yanzu kam mun yanke kauna a gwamnatin Buhari

Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo, haka aka sako 'yan GSC Kagara
Gwamnan Neja: Bamu biya kudin fansa ko kobo, haka aka sako 'yan GSC Kagara Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa da wadanda aka sacen, Bello ya ce "dabaru da yawa" na gwamnati sun shiga cikin tabbatar da sakinsu cikin koshin lafiya da kuma jigilar wadanda aka sacen daga hannun masu satar mutanen zuwa babban birnin jihar.

Gwamnan Neja ya lura cewa hukumomin tsaro, da masu rike da sarautun gargajiya, da kuma 'yan bangan cikin gida suna da hannu wajen tabbatar da sakin wadanda lamarin ya rutsa da su cikin koshin lafiya.

“Bamu biya fansa ba. Duk da haka, mun shiga jigilar kayan aiki da yawa saboda dole ne mu hada kungiyoyi da yawa - har ma da dabaru- don dawo dasu, da kuma sasanta masu ruwa da tsaki.

"Ina magana ne kan hukumomin tsaro, 'yan bangan cikin gida, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki." In ji shi.

Ya kuma lura da cewa sakin wadanda aka sacen aiki ne mai wahala ga gwamnatinsa, ya kara da cewa suna farin ciki da kokarin da aka yi.

"Aiki ne mai matukar wahalar gaske, mai matukar bukata, kuma a karshe, muna farin cikin sakamakon da aka samu," in ji shi.

KU KARANTA: Tawagar samu gyaran wutar lantarki a Borno ta ci karo da nakiyar da ISWAP suka dasa

A wani labarin, Jami'an tsaro da wata kungiyar tsaro ta sa kai sun fara neman 'yan mata sama da 400 da 'yan bindiga suka sace a safiyar ranar Juma'a daga makarantar su da ke Jengebe, jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

An sace 'yan matan makarantar ne lokacin da 'yan bindigan suka afkawa makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati ta Jangebe sannan daga baya suka yi awn gaba da daliban.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.