Dattawan Arewa: Yanzu kam mun yanke kauna a gwamnatin Buhari

Dattawan Arewa: Yanzu kam mun yanke kauna a gwamnatin Buhari

- Kungiyar Dattawan Arewa sun bayyana yanke kauna da tsaron da gwamnatin Buhari ke ikrarin yi

- Sun nuna rashin jin dadinsu ga yadda gwamnati ke rikon sakainar kashi da matsalar tsaro a Arewa

- Sun kuma shawarci gwamnoni da su dauki matakan da suka dace don ganin sun inganta tsaro a jihohinsu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce duk da tabbaci daga gwamnatin tarayya cewa za ta kawo karshen ‘yan bindiga da sace-sacen mutane; rayukan 'yan Najeriya na kara shiga cikin hadari, The Cable ta ruwaito.

Taron na mayar da martani ne kan batun sace-sacen mutane, musamman sace 'yan makaranta mata 317 daga Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati dake Jangebe a karamar hukumar Talata-Mafara, a jihar Zamfara.

A wata sanarwa daga Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai da lamuran yau da kullum na kungiyar, dattawan sun ce 'yan Najeriya sun "yanke kauna cewa gwamnati za ta sauya nasarorin da masu laifi ke samu kan talikan 'yan kasa da basa aikata laifi".

Dattawan sun yi kira ga gwamnonin jihohi, musamman daga yankin arewa, da su binciki hanyoyin tsarin mulki na kafa tsarin da zai kubutar da al'umma.

KU KARANTA: Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu

Dattawan Arewa: Yanzu kam mun yanke kauna a gwamnatin Buhari
Dattawan Arewa: Yanzu kam mun yanke kauna a gwamnatin Buhari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sun kuma roki gwamnoni da su bincika tare da warware matsalolin da ke taimakawa yaduwar ta'addancin a matakan gida da na al'umma.

"Ya bayyana karara cikin raɗaɗi cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya yin amfani da iko ko damar ta iyakance 'yan Najeriya daga masu aikata muggan laifuka ba," in ji kungiyar.

“Duk da tabbaci daga gwamnatin tarayya cewa za ta kawo karshen 'yan bindiga da sace-sacen mutane, rayuwar dan Najeriyar na kara shiga cikin hadari a kowace rana.

"Kuma 'yan kasa sun yanke kauna cewa gwamnatoci za su sauya nasarorin da mai laifi ke samu kan ‘yan kasa marasa aikata laifi."

“Kungiyar na ba da shawara musamman ga gwamnonin Arewa da su binciko duk hanyoyin da doka ta tanada don inganta tsaron 'yan kasa.

“Yayin da ya kamata su inganta goyon bayansu ga sojoji, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro, ya kamata su binciko hanyoyin da za su ba su karin ikon kiyaye ‘yan kasa cikin tsarin mulki wanda ya baiwa jihohi iko su kafa tsarin 'yan sanda.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnoni da su samar da "wadanda ke da kwarewa yadda ya kamata a fannin sanin gandun daji a matsayin wani lamari na gaggawa a kasar.

"'Yan bindigan da suka ki mika wuya don sasantawa da dakatar da aikata laifuka ya kamata a bi da su daidai da dokokin kasa."

Har ila yau, kungiyar ta ce tana bakin ciki da mummunan tasirin satar da aka yi a fannin ilimi.

Kungiyar ta nemi iyaye da kada su karaya game da tura yaransu zuwa makaranta yayin da suke kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki tsauraran matakai don tabbatar da tsaro a makarantu.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya da Manoma: Mu Fulani ba 'yan ta'adda bane, in ji Sarkin Musulmi

A wani labarin, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya roki Fulani makiyaya da kada su dauki bindiga AK-47 kuma su kasance cikin lumana.

Gwamnan, ya yi wannan rokon a jawabinsa a wajen kaddamar da allurar rigakafin dabbobi na shekara-shekara ta 2020/2021 da aka gudanar a Galambi Cattle Ranch dake Bauchi, ranar Laraba, ya bayyana Fulani a matsayin masu tawali’u, masu sauƙin kai, da kawaici.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel