Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara

Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara

- Jami'an tsaro a yankin jihar Zamfara sun tsunduma neman daliban da aka sace a jihar ta Zamfara

- Wasu jami'an sa kai su ma ba a bar su a baya ba wajen ganin cewa an ceto daliban da aka sace

- A Najeriya ana ci gaba da sace-sacen dalibai, wanda ke jawo cece-kuce tsakanin al'umma a kasar

Jami'an tsaro da wata kungiyar tsaro ta sa kai sun fara neman 'yan mata sama da 400 da 'yan bindiga suka sace a safiyar ranar Juma'a daga makarantar su da ke Jengebe, jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

An sace 'yan matan makarantar ne lokacin da 'yan bindigan suka afkawa makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati ta Jangebe sannan daga baya suka yi awn gaba da daliban.

Majiyoyi da yawa sun shaida wa walikin HumAngle cewa adadin 'yan matan makarantar da aka sace zai iya haura 417 yayin da wasu suka ce adadin na iya fin haka,

Jangebe wani yanki ne na karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

Mun samu labarin cewa jami’an tsaro da ‘yan banga na yankin na yunkurin ceto daliban.

KU KARANTA: Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu

Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara
Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara Hoto: The Guardian
Source: Twitter

Kabiru Sani, mataimakin shugaban kungiyar Muryar Talaka a jihar Zamfara, wanda aka sace yaransa uku, ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun kutsa ta kofar makarantar tare da nuna fin karfin mai tsaronta kafin su sace daliban.

Wani malami a makarantar ya kuma shaida wa Aminiya cewa bayan satar, dalibai basu wuce 50 suka saura a makarantar wacce ke da yawan dalibai sama da 600.

“Lokacin da 'yan bindigan suka yi wa makarantar kawanya, sai da suka far wa sojojin da ke yankin kafin su samu shiga makarantar. Wasu mutane sun gaya mana cewa sun ajiye motoci a gefen makarantar,” malamin ya fada.

Satar daliban makarantar ya faru ne 'yan makonni kadan bayan an kashe wani dalibin makaranta kuma aka sace wasu dalibai 27 da wasu ma’aikata da danginsu a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati a jihar Neja, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Satar farko da aka yi a wata makaranta a Najeriya ta faru ne a jihar Borno, inda Boko Haram suka sace sama da daliban makarantar Sakandaren Gwamnati ta Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014.

Shekaru huɗu bayan haka, Daular Islama ta Yammacin Afirka (ISWAP) ta sace ɗalibai 119 daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta 'yan mata dake Dapchi, Jihar Yobe.

A watan Disambar 2020, an sace dalibai sama da 300 daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Kankara, Jihar Katsina.

KU KARANTA: Kawai gwamnati ta kame Sheikh Gumi ta bincikeshi kan hada kai da 'yan bindiga, wasu 'yan Najeriya

A wani labarin, Wani tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dokta Obadiah Mailafia, ya ce da yawa daga cikin ‘yan fashin da ke addabar kasar nan wasu mutane ne suka dauki nauyin su da ke son su ture tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga mulki ta kowane hali.

Mailafia ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Alhamis.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel