Wadanda suka so Jonathan ya fadi zabe ne ke daukar nauyin 'yan bindiga, Mailafia

Wadanda suka so Jonathan ya fadi zabe ne ke daukar nauyin 'yan bindiga, Mailafia

- Wani tsohon mataimakin babban bankin Najeriya ya caccaki wasu da yake zargin masu daukar nauyin ta'addanci

- Yace, asalin 'yan bindiga wasu dake son ture gwamnatin shugaba Jonathan a zaben shekarar 2015 ke daukar nauyinsu

- Hakazalika yace, ba daidai bane ake kwatanta 'yan bindigan da tsagerun Neja Delta ba, domin basu da hadi

Wani tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dokta Obadiah Mailafia, ya ce da yawa daga cikin ‘yan fashin da ke addabar kasar nan wasu mutane ne suka dauki nauyin su da ke son su ture tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga mulki ta kowane hali.

Mailafia ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Alhamis.

Ya ce, “A lokacin zaben 2015 sun shigo da dubban 'yan kasashen ketare cikin kasar nan, suna ba su makamai saboda lamari ne na idan Goodluck Jonathan bai mika wuya ba, za a yi yaki. Sun kasance a shirye don yakin basasa; ba su kasance a shirye don zaman lafiya ba.

"Tabbas, Jonathan ya mika musu mulkin, sannan kuma suka juya baya ga maharan sai maharan suka ce 'ku duba, kun kawo mu nan kuma har yanzu muna nan'."

KU KARANTA: Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu

Wadanda suka so Jonathan ya fadi zabe ne ke daukar nauyin 'yan bindiga, Mailafia
Wadanda suka so Jonathan ya fadi zabe ne ke daukar nauyin 'yan bindiga, Mailafia Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Mailafia, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben da ya gabata, ya ce ya kuma gamsu cewa wasu ketare na goyon bayan 'yan bindigan.

“Akwai wasu manyan kasashen duniya da suke son rusa kasarmu. Abinda nayi imani dashi kenan.

"Akwai wata kwantaina dauke da makamai da aka shigo da su daga kasar Turkiyya. Wani lokaci a aka kawo wasu daga kasar Iran. Amma ba wanda ya kara yin bincike haka maganar ta wuce; karshenta ke nan,” inji shi.

Mailafia, a shekarar da ta gabata hukumar DSS da 'yan sanda sun gayyace shi ya bada bayanin ikirarinsa na cewa wani gwamnan arewa ne kwamandan 'yan Boko Haram.

Shi ma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin na CBN bai amince da yadda Sheikh Ahmad Gumi yake tunkarar batun afuwa ga 'yan bindiga ba.

Mailafia ya ce ba daidai ba ne a yi irin wannan afuwa ga 'yan iska makasa sannan kuma ba a yi wa wadanda aka cuta adalci ba, yana mai cewa 'yan bindigan basu da manufar da ta wuce rusa al'umma.

Ya yi ikirarin cewa gamsar da 'yan bindigan ba zai taba aiki ba kamar yadda a cewarsa tsagerun Neja Delta da 'yan ta'addan da ke addabar kasar abubuwa ne daban da basu da alaka.

“Ban yi imani da cewa za a iya kwatanta tsagerun Neja Delta da 'yan ta’adda ba. Wadannan mutane ('yan ta'adda) ba 'yan bindiga bane. 'Yan bindiga barayi ne na gama gari ko kuma 'yan daba. ‘Agbero’ ’yan bindiga ne.

"Wadannan mutanen dauke da manyan makamai da bindigun harbo jirgi ba 'yan bindiga bane. 'Yan ta'adda ne.

"Sun kashe, sun raunata, sun yi fyade kuma sun yi barna sosai," in ji Mailafia.

KU KARANTA: An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki

A wani labarin, 'Yan ta'addan Neja-Delta, wadanda suka bar bindigoginsu sama da shekaru biyar, sun sake yin fito-na-fito inda suka yi barazanar sake daukarta su kai hari Lagos da Abuja.

Biranen biyu sune cibiyoyin kasuwanci da tafiyar da mulkin ƙasar, Daily Trust ta kawo.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel