An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki

An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki

- Wasu yara a jihar Legas sun garkame mahaifinsu a daki na tsawon shekara guda a gidansa

- 'Yan sanda sun kame yaran tare da turasu zuwa cibiyar bincike don gudanar da bincike da kyau

- An zarce da mahaifin nasu zuwa asibiti domin ya samu murmurewa da kuma bincika lafiyarsa

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas sun cafke Saidat Kazeem da Fatimo Onakoya bisa zargin hada baki da wasu 'yan uwa wajen tsare mahaifinsu, Surajudeen Jaji, a wani daki na tsawon watanni 12 a gidansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamun Saidat da Fatimo ga majiyarmu ranar Laraba tare da 'yan sanda da ke aiki a sashin Ejigbo da rakiyar wani memba na kwamitin kare hakkin dan Adam, Abdulganiyu Salaudeen.

Adejobi ya ce, za a tura Saidat da Fatimo zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar dake Panti, Yaba, don gudanar da bincike cikin hikima, yayin da ake kokarin cafke wadanda suke da hannu cikin aikata laifin.

An ruwaito cewa sun tsare mahaifin nasu cikin wani daki a cikin gidansa ne saboda zargin cewa yana shirin sayar da kadarorinsa.

KU KARANTA: Rikicin makiyaya: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani kada su dauki AK-47

An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki
An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki Hoto: First News
Asali: UGC

Don haka saboda su hana shi aiwatar da shirinsa, an ce yaran sun umarci kuyangarsa da ta hana maziyarta samun damar zuwa wurinsa, kuma duk lokacin da aka tambayesu game da inda Jaji yake, yaran kan ce sun tsare shi ne bisa dokar COVID-19.

Salaudeen ya fadawa majiya cewa rikici ya fara ne tsakanin Jaji da dangin sa lokacin da yaransa suka kori wata kuyangarsa, mai suna Adija, wacce ke aikin kula da shi da matar sa, Rashidat, bisa zargin cewa tana aikata lalata tare da mahaifinsu.

An ce yaran sun kuma kwace wayar Jaji don hana shi tuntuɓar kowa, ciki har da Adija.

Daya daga cikin yaran Jaji, Titi, ta musanta zargin tsare mahaifin nasu, tana mai cewa, “Ban san dalilin da ya sa ta (Adija) take yada zargin karya cikin mutane daban-daban cewa mun kulle mahaifinmu ba.

"Me yasa zamu yiwa mahaifinmu irin wannan kuma me yasa musamman Adija ce ta damu game da mahaifinmu? Mahaifiyarmu ma tana gida daya tare damu dashi.”

A lokacin da ake ceton Jaji ranar Talata, an ji shi a cikin wani bidiyo yana cewa, “Ina son 'yanci na, amma ina son wani tabbaci, ‘ya’yana ba za su shiga gidan nan ba har sai na mutu. Su kuma tafi da mahaifiyarsu duk inda za su.”

'Yan sanda, Salaudeen da Shugaban LCDA daga baya sun kai Jaji zuwa cibiyar lafiya a Ejigbo don jiyya.

KU KARANTA: Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro a Najeriya, Amina Mohammed

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Talata sun afkawa karamar hukumar Matazu da ke cikin jihar Katsina inda suka yi garkuwa da Hajiya Rabi, surukar shahararren attajirin dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Wata majiya daga danginsa, wacce ba ta so a bayyana sunan ta ba ta shaida wa jaridar Punch a Kano a wata hira ta wayar tarho cewa ‘yan bindigan wadanda suka iso garin da misalin karfe 1 na daren jiya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.