Fatima Atiku ta musanta rade-radin da ake na sabunta rijistarta a APC

Fatima Atiku ta musanta rade-radin da ake na sabunta rijistarta a APC

- Dr. Fatima Atiku Abubakar ta musanta rade-radin sabuntar rijistar APC da aka ce tayi

- Ta sanar da cewa a halin yanzu bata da wata alaka da jam'iyyar siyasa kowacce iri

- A cewarta, ta yi rijistar APC a 2015 ne saboda za ta yi aikin kwamishinan lafiya a jihar

Diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Dr. Fatima Atiku Abubakar ta karyata ikirarin cewa ta yi sabunta rijistar zama cikakkiyar 'yar APC.

A wata takarda da ta fitar da kanta kuma ta saka hannu sannan ta baiwa manema labarai a ranar Laraba, Dr.Fatima ta ce zamanta 'yar APC a baya saboda bukatar gwamnatin Bindo na jihar Adamawa ne, Vanguard ta wallafa.

"Akasin rahotanni da ke yawo, ban sabunta rijistar APC ba. A 2015 lokacin da aka nada ni kwamishinan lafiya ta jihar Adamawa yasa na koma jam'iyyar mai mulki. Hakan ya zama dole in zan yi aikin.

KU KARANTA: Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

Fatima Atiku ta musanta rade-radin da ake na komawarta APC
Fatima Atiku ta musanta rade-radin da ake na komawarta APC. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

"Tun bayan kammala aikin a matsayin kwamishina, ina aiki ne na kaina ba tare da wata jam'iyya ba. Na sha mamaki da naji labarin cewa na sabunta rijistar APC."

"Domin gujewa waswasi, ban sabunta rijistar APC na ba wanda nayi saboda aikin da zan yi a 2015. Ina Abuja, ban je Jada ba inda ake cewa na sabuunta rijistar. Sa hannun da ke kan takardar da ake yadawa ba nawa bane." takardar tace.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojojin Najeriya sun kwato garin Marte daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce nan babu dadewa za ta fara shari'ar wasu mutum 5,000 da ake zargi da zama 'yan ta'addan Boko Haram kuma suna tsare a gidajen gyaran halin kasar nan.

Darakta janar na kungiyar shari'a, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Borno, Babagana Zulum a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Abubakar ya bayyana barikin Giwa da ke Maiduguri, gidan gyaran hali na Kainji a matsayin wuraren da aka adana wadanda ake zargin da ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel