'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata wasu 3 a Neja

'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata wasu 3 a Neja

- Wasu 'yan bindiga sun sheke dan sanda mai mukamin sifeta daga saman bishiya

- An gano cewa 'yan sandan na baiwa matafiya kariya ne a babbar hanyar Minna- Suleja

- A take dan sandan ya mutu bayan ruwan harsasai da aka yi mishi sannan wasu 3 suka jigata

'Yan bindiga sun samo wani sabon salo na kaiwa jama'a farmaki a jihar Neja.

Wasu gungun 'yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari inda suka kashe dan sanda mai mukamin sifeta daga saman bishiya tare da raunata wasu 'yan sandan uku.

An gano cewa an tura 'yan sandan ne domin baiwa matafiya da ke kan babbar hanyar Minna zuwa Suleja kariya. Amma sai aka kai musu farmaki a ranar Talata da yammaci a wurin Kaffinkoro.

An gano cewa 'yan sandan na tsaye ne inda suke sintiri a kan babbar hanyar lokacin da 'yan bindigan suka yi musu ruwan harsasai daga saman bishiya.

KU KARANTA: Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi

'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata mutum 3 a Neja
'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata mutum 3 a Neja. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: UGC

A take sifetan ya fadi matacce yayin da sauran ukun suka jigata, Vanguard ta wallafa.

Sunan sifetan Mohammed Mohammed kuma tuni aka birne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar yayin da sauran ukun ke asibitin kwararru na IBB da ke Minna.

Wani kanin mahaifin sifetan 'yan sandan da ya rasu kuma tsohon kakakin majalisar jihar Nejan, Ndanusa Hassan, ya tabbatar da birne mamacin da aka yi a ranar Laraba.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce nan babu dadewa za ta fara shari'ar wasu mutum 5,000 da ake zargi da zama 'yan ta'addan Boko Haram kuma suna tsare a gidajen gyaran halin kasar nan.

Darakta janar na kungiyar shari'a, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Borno, Babagana Zulum a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Abubakar ya bayyana barikin Giwa da ke Maiduguri, gidan gyaran hali na Kainji a matsayin wuraren da aka adana wadanda ake zargin da ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel