Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa

Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa

- Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kashe makudan kudade don sayen barkonon tsohuwa

- Majalisar dattawan sun kuma amince da ware wasu kudade domin sayen makamai da alburusai

- Majalisar ta bayyana hakan a matsayin bai wa 'yan sanda kwarin gwiwa su gudanar da ayyukansu

A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da kashe Naira biliyan 11.3 (11,352,457,101.70) a matsayin kasafin kudin Asusun Dogaro na ’Yan sandan Nijeriya (NPTF) na kasafin kudin shekarar 2020.

Kimanin N1.3bn (1,362,814,243) daga cikin kudin da aka kasafta domin siyan barkonon tsohuwa. An ware kimanin Naira biliyan daya domin sayen makamai da alburusai, Premium Times ta kawo.

Amincewar ta biyo bayan la'akari da daukar rahoton da ya dace na kwamitin majalisar dattijai da na wakilai kan harkokin 'yan sanda. Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Haliru Jika ne ya gabatar da rahoton.

Amincewar majalisar dattijan na zuwa ne mako guda bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura kasafin kudin ga majalisar dattawan domin dubawa da kuma amincewa. Aiwatar da kasafin kudin zai fara a ranar 30 ga Afrilu, 2021.

KU KARANTA: Masu bukulun na sayi jirage har 3 sai sun mutu a bakin ciki, Fasto Suleiman

Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa
Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mista Jika a jawabinsa ya ce wannan shi ne kasafin farko na NPTF, tun lokacin da aka kafa dokar a shekarar 2019.

Kashi 0.5 cikin 100% na yawan kuɗaɗen shiga da aka samu a Asusun Tarayya da kuma 0.5% cikin 100% na adadin Haraji da aka tura su zuwa asusun NPTF; sauran hanyoyin samun kudin shiga kamar yadda aka tsara a dokar NPTF ba su kawo kudi ba, in ji shi.

Da yake bayar da bayanin rarar bangaren kasafin kudin, dan majalisar ya ce ana sa ran kudin shiga Naira biliyan 35 (N34,984,314,243) yayin da aka ware Naira biliyan 11.3 (N11,354,457,101.70) don kashewa hidimar.

Ya bayyana cewa ragowar N23.6 biliyan (N23,631,857,141.30) na 2020 za a kwashe su zuwa kasafin 2021 na NPTF.

Don haka, ya yi kira ga NPTF da ta hanzarta aiki kan aiwatar da kasafin kudin 2020 domin cimma wa'adin 30 ga Afrilu.

A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce amincewa da kasafin na NPTF zai “taimaka wa 'yan sanda su kara karfinsu kuma ba shakka, zasu samar da ingantattu da nagartattun ayyuka a duk fadin kasar.”

"Wannan na daga cikin fa'idodin abin da muka tattauna a nan - Asusun Amintattun 'Yan Sanda - kuma na tabbata cewa Majalisar Dokoki ta Kasa za ta ci gaba da tallafa wa jami'an tsaronmu don kyakkyawan aiki," in ji shi.

KU KARANTA: Saura kwanaki 10 allurar rigakafin Korona ta iso Najeriya, Ministan Lafiya

A wani labarin, Majalisar dattijai ta fara tantance sabon Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, Vanguard ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.