Masu bukulun na sayi jirage har 3 sai sun mutu a bakin ciki, Fasto Suleiman
- Fasto mai jiragen sama 3 ya caccaki masu suka da yi masa hassada don ya mallaki jirage uku
- Ya kuma yi danasanin cewa ba ya son Korona ta kare saboda yana jin dadin lokacin Korona
- Hakazalika yace duk masu masa bakin ciki sai sun mutu da haushi, yana mai fada cikin fushi
Fasto Johnson Suleman ya la'anci mutanen da suka fusata saboda ya sayi jirgi na uku a lokacin kullen COVID-19, PM News ta ruwaito.
Babban mai lura da Omega Fire Ministries International, a wani bidiyo, ya ce ya sayi jirgi na uku a yayin barkewar annobar COVID-19, wanda ya jefa kasar cikin koma bayan tattalin arziki.
Malamin majami'an ya ci gaba da cewa yana addu'ar kada wannan annobar ta kare saboda yana samun ci gaba yana kuma hutawa.
KU KARANTA: An kame wasu yara da suka garkame mahaifinsu na tsawon watanni 12 a daki
Ya ce, “A lokacin COVID (annoba) na sayi jirgi; na uku. Ina da uku yanzu. Ina ta addu'ar kada COVID-19 ya ƙare saboda ina hutawa. Yayin da mutane suke gunaguni, matata ta tambaya, ‘Shin rayuwa za ta iya zama mai daɗi haka?’ Shin ina magana da wani a nan ne?
“Babu damuwa. Na karanta a Intanet cewa akwai jita-jita da ke yawo cewa ina da wata na'ura da take buga kuɗi. Ina son wannan jita-jita. Suna cewa, ‘Ya kamata a bincike shi. Yana da injin da yake buga kudi ’.
“Wani ya tambaya ko gaskiya ne ni kuma na ce gaskiya ne. Suka ce, 'Yana da haɗari fa'. Na ce ban sani ba yana da haɗari saboda na riga na sayi injin. Lokacin da kake magana cikin harsuna, kana buga kudi ne."
Sai dai, a cikin sabon bidiyon da ya bayyana a yanar gizo, Fasto Suleman ya ce ya yi kuskure da cewa "Ina ta addu'ar kada COVID-19 ta kare."
Amma, ya kara da cewa wadanda suka fusata saboda ya sayi wani jirgi mai zaman kansa "zasu mutu"
KU KARANTA: Ya kamata a koyar da yara da asalin yarensu, ba yaren aro ba, inji wani marubuci
A wani labarin, Ministan lafiya Osagie Ehanire ya fada a Lagas jiya cewa Najeriya na iya samun allurar rigakafin COVID-19 nan da kwanaki 10 masu zuwa, The Nation ta ruwaito. '
Ministan ya ce "An gaya mana cewa a karshen wannan watan, wato kimanin kwanaki 10 kenan daga yanzu, za mu sami alluran."
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng