Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro a Najeriya, Amina Mohammed

Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro a Najeriya, Amina Mohammed

- Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar dinkin duniya ta shawarci gwamnatin Najeriya

- A cewarta, ya kamata Najeriya ta bada karfi wajen zuba hannun jari kan matasan kasar

- Ta bayyana zuba hannun jari kan matasa a matsayin hanyar kawar da matsalar rashin tsaro

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed ta roki Gwamnatin Tarayya ta kara sanya jari a kan matasa a matsayin wata hanya ta magance rashin tsaro, a rahoton Channels Tv.

Da take magana yayin ziyarar girmamawa ga Ministan Harkokin Wajen Najeriya Mista Geoffrey Onyeama, Misis Amina ta lura cewa ya kamata a bai wa matasa da sauran ‘yan Nijeriya wani abin da za su sa ido domin bayar da gudummawa ga ci gaban kasar.

KU KARANTA: Tsadar kudin wutan lantarki: Muna biyan ninki ukun abinda muke biya a baya, 'yan Najeriya

Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro, Amina Mohammed
Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro, Amina Mohammed Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Ta kara da cewa saka hannun jarin da take magana ya kamata ya zama a bangarori kamar bunkasa kwarewa, ilimi da ayyuka da ke karfafa shugabanci a matakin kananan hukumomi.

Najeriya a tsawon shekaru ta kasance cikin hargitsi da tashin-tashina na yawaitar aikata manyan laifuka irinsu sace-sace, hare-hare da kuma matsalar Boko Haram.

Amina Mohammed ta lura cewa hanya mafi sauki wajen magance damauwar rashin tsaro a kasar shine zuba hannun jari kan matasa ta fannoni da dama.

KU KARANTA: CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin

Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro, Amina Mohammed
Zuba jari kan matasa ne kadai mafita ga rashin tsaro, Amina Mohammed Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

A wani labarin, Shugaban, Kungiyar Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwumi Adesina, ya ce kimanin mutane miliyan 87 ke rayuwa cikin matsanancin talauci a Najeriya, a rahoton Aminiya.

Ya fadi haka ne jiya a Akure yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken “From Federal Fatherism to a Commonwealth” a matsayin laccar ƙaddamarwa a karo na biyu na Gwamna Oluwarotimi Akeredolu.

Ya ce: "Wannan talaucin da ya tabarbare" ya sanya kasar "ta kasance mai matukar fuskantar barazanar zamantakewa da siyasa" kuma ta samar da "kofa ga masu adawa da zamantakewar al'umma da daukar ma'aikata daga 'yan tawaye da 'yan ta'adda".

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel