‘Yan bindiga sun sace surukar shahararren dan kasuwa Dahiru Mangal

‘Yan bindiga sun sace surukar shahararren dan kasuwa Dahiru Mangal

- 'Yan bindiga a jihar Katsina sun yi awon gaba da surukar Alhaji Dahiru Barau Manga

- 'Yan bindigan sun dira gidan surukar tasa ne cikin dare da misalin karfe 1 a garin Matazu

- 'Yan bindigan har zuwa yanzu basu tuntubi dangin surukar tasa ba, kuma ba a ji labari ba

Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Talata sun afkawa karamar hukumar Matazu da ke cikin jihar Katsina inda suka yi garkuwa da Hajiya Rabi, surukar shahararren attajirin dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Barau Mangal.

Wata majiya daga danginsa, wacce ba ta so a bayyana sunan ta ba ta shaida wa jaridar Punch a Kano a wata hira ta wayar tarho cewa ‘yan bindigan wadanda suka iso garin da misalin karfe 1 na daren jiya.

Ta kuma ce kai tsaye suka tafi gidan da su Hajiya Rabi suke inda suka tattarata suka yi awon gaba da ita zuwa inda ba a sani ba.

A cewar majiyar, kafin sace Hajiyar, ‘yan bindigar sun sace gaba da surukin danta, wanda ake kira da Buhari Muntari a cikin Garin Katsina.

Majiyar ta ce "'Yan bindigar sun kasance kafin su tafi Matazu sun sace surukin dan Hajiya Rabi a Katsina.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Oyo ya bada umarnin sake bude kasuwar Sasha a yau

‘Yan bindiga sun sace surukar shahararren dan kasuwa Dahiru Mangal
‘Yan bindiga sun sace surukar shahararren dan kasuwa Dahiru Mangal Hoto: Liberty Tv/Radio
Asali: UGC

Da aka tuntube shi, mijin wanda aka sace din, Alhaji Muntari Masanawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho a Kano ranar Talata.

Muntari, wanda shi ne mai rike da sarautar ‘Sarkin Yaki’ a Matazu, ya ce ‘yan bindigan da suka je gidansa da misalin karfe 1.30 na dare sun tayar da matarsa suka dauke ta a kan babur.

Ya ce ‘yan bindigar sun nemi matarsa ta biyu da ta fito da duk kudaden da take da su amma ta ce musu ba ta da kudi.

Lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, ASP Isah Gambo, ya ce ba shi da masaniya game da lamarin.

Amma, ya fadawa jaridar Punch cewa zai samu labarin daga ofishin 'yan sanda na yankin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, har yanzu basu kira danginta ba.

KU KARANTA: Na tabbata daliban makarantar Kagara na dajin Birnin Gwari, in ji Gwamna Matawalle

A wani labarin, Akwai alamu masu karfi a ranar Litinin cewa rashin jituwa tsakanin ‘yan fashi a jihar Neja na jinkirta sakin daliban 27 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati 15, da aka sace a ranar Laraba.

Wata majiya daga gwamnati, wacce ta bayyana wa jaridar Punch, ta ce 'yan bindigar da suka yi garkuwar ba su amince da tattaunawar da sukayi da wakilan gwamnatin ba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.