Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 18 a Kaduna

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 18 a Kaduna

- Yan bindiga sun kai farmaki kananan hukumomin Igabi da Chikun a jihar Kaduna

- Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane da dama tare da kona wasu gidaje

- Sai dai kuma, jami'an tsaro sun yi nasarar kashe da dama daga cikin maharan

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun halaka akalla mutane 18 a wani hari da suka kai wasu yankunan jihar Kaduna.

A bisa ga wata sanarwar daga gwamnatin Kaduna, ta ce an kai hare-haren ne a kananan hukumomin Igabi da Chikun, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zargin ta'addanci: Gwamnan Bauchi ya ƙallubalanci Ortom da ya kawo hujja

Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 18 a Kaduna
Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 18 a Kaduna Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

Maharan sun kuma sace mutane da dama tare da kone gidaje a kauyen Anaba da ke cikin karamar hukumar Igabi.

Hakazaika, baya ga garuwa da mutune yan bindigar sun kuma saci shanu a kauyen Barinje da ke cikin karamar hukumar Chikun.

Sanarwar ta ce kuma jami’an tsaron Najeriya sun kashe yan bindiga da dama.

A gefe guda, tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce za a iya magance barazanar tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ta hanyar yin dogon shiri.

Channels TV ta ruwaito cewa a Babangida, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, 23 ga Fabrairu, ya ce kasar za ta iya shawo kan matsalar tsaro idan wadanda ke kan mukamai suka yi shiri yadda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: 2023: Hadimin Tsohon Shugaban kasa ya karyata rade-radin takara da komawar Jonathan APC

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce kawar da barazanar da masu satar mutane, 'yan fashi, da masu tayar da kayar baya ke yi yana bukatar babban shiri, ya kara da cewa ba shiri bane na wani dan gajeren lokaci.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel